'Na Shiga Motar Tinubu': Tsohon Ɗan Majalisa Ya Watsar da PDP, Ya Kama Layin APC

'Na Shiga Motar Tinubu': Tsohon Ɗan Majalisa Ya Watsar da PDP, Ya Kama Layin APC

  • Daya daga cikin kusoshin jam'iyyar PDP a jihar Delta, kuma tsohon dan majalisar wakilai, Nicholas Ossai ya sauya sheka zuwa APC
  • A taron manema labarai da ya gudanar, Hon. Nicholas Ossai ya ce ya saki layin PDP a yanzu domin marawa Shugaba Bola Tinubu baya
  • Tsohon dan majalisar ya ba shugaba Tinubu tabbacin cewa zai yi aiki tare da gwamnatinsa domin kai Najeriya zuwa tudun-mun-tsira

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon dan majalisar wakilai, Nicholas Ossai, ya sanar da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki a kasa.

Hon. Nicholas Ossai, wanda ya wakilci Ndokwa ta Gabas/Ndokwa ta Yamma/Ukwuani ya ce ya sauya sheka domin mara wa Bola Tinubu baya.

Tsohon dan majalisar wakilai ya bayyana dalilin ficewa daga PDP, ya koma APC
Tsohon dan majalisar wakilai ya fice daga PDP, ya koma APC domin taimakawa gwamnatin Tinubu. Hoto: @YIAGA, @officialABAT
Asali: Twitter

Tsohon dan majalisa ya bar PDP, ya koma APC

Kara karanta wannan

Me yake shiryawa?: Na hannun damar Peter Obi da ya fice daga LP ya gana da Atiku

Da yake jawabi a taron manema labarai a ranar Alhamis, Ossai ya ce yanzu ya shiga motar Tinubu domin taimaka masa wajen kawo ci gaba a Najeriya, inji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon dan majalisar ya ce manufofin Tinubu suna da matukar muhimmanci wajen bunkasa kasa, musamman la’akari da irin nasarorin da ya samu tun yana gwamnan Legas.

Hon. Ossai ya caccaki PDP, yana mai cewa jam’iyyar ta rasa alkibla, don haka ya yanke shawarar komawa APC domin ci gaba da ayyukan raya kasa.

“Tutar PDP ta karye, kuma wadanda ya kamata su gyara ta sun gaza. Saboda haka, na yanke shawarar bin Tinubu,” in ji Ossai.

Ya bayyana kwarin gwiwa cewa APC za ta lashe zaben 2027 a jihar Delta sakamakon nasarorin da jam’iyyar ke samu a matakin kasa.

Ossai ya jinjinawa shirin Tinubu kan noma

Hon. Ossai ya yabawa manufofin tattalin arziki da noma na gwamnatin tarayya, yana mai cewa matakan da aka dauka sun fara haifar da sakamako mai kyau.

Kara karanta wannan

Tsohon makusancin Peter Obi ya hango rugujewar LP, ya fadi makomarsa a 2027

Tsohon dan majalisar ya ce:

"Ku duba harkar noma, dukkanin gwamnonin APC na kokarin kawo sauyi a harkar abinci. Har ma an rage yawan hauhawar farashi."

Ya ce kasashen duniya sun fara girmama Najeriya saboda nagartar shugaba Tinubu, wanda ya kira shi gwarzon da yake so ya yi koyi da shi.

Ossai ya fara wakiltar mazabar Ndokwa East/Ndokwa West/Ukwuani a majalisar wakilai a 2011, sannan aka sake zabarsa a 2015 da 2019 karkashin PDP.

APC ta yi maraba da tsohon dan majalisar

Jam'iyyar APC ta yi maraba da tsohon dan majalisar wakilai, Hon. Ossai
APC ta ji dadi da Hon. Ossai, tsohon dan majalisar wakilai ya shiga jam'iyyar. Hoto: @YIAGA
Asali: Twitter

Da yake tarbar Ossai, sakataren APC na kasa, Sanata Ajibola Basiru, ya ce wannan sauya shekar yana nuna cewa 'yan Najeriya sun gaji da PDP.

The Punch ta rahoto Basiru ya ce APC na aiki tukuru don farfado da Najeriya tare da janyo 'yan siyasa masu kwarewa domin ci gaba da samun nasara a zabukan kasar.

Ya ce manufofin Tinubu sun riga sun fara yin tasiri, kuma ‘yan Najeriya za su sake zabarsa a 2027 domin cigaba da wannan tafiya.

Kara karanta wannan

'Ya ci burin kawar da Kiristocin Kaduna': Hadimin Jonathan ya zargi El Rufai

Fubara ya ja ra'ayin 'yan PDP sun bi Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwaman Ribas, Siminalayi Fubara ya ja ra'ayin wasu shugabannin PDP a jihar sun koma goyon bayan shugaba Bola Tinubu.

Chief Abiye Sekibo, tsohon ministan sufuri, ya sanar da cewa Fubara ya shawo kan jagororin jihar suka juyawa Atiku Abubakar baya, yana mai nuna goyon baya ga Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel