Jerin 'yan majalisar wakilai da suka fi kawo kudirorin samar da ci gaba a kasa
An yanke hukuncin cewa, Abbas Tajuddeen da Tahir Monguno, su ne 'yan majalisar wakilai guda biyu da suka fi sa'o'insu kawo mafi yawan kudirori domin ci gaban kasa.
Honarabul Tajuddeen wanda ya ke wakiltar mazabar Zaria a zauren majalisar tarayya, ya kawo kudirori 59, yayin da takwaransa Monguno na jihar Borno, ya kawo kudirori 40.
Kamar yadda rajistar majalisar dokoki ta tarayya ta nuna, Femi Gbajbiamila, kakakin majalisar wakilai na yanzu, ya fi kowane dan majalisa kawo yawan kudirorin da tuni an shigar da su cikin doka.
Sauran 'yan majalisar da suka kawo tarin kudirori domin ci gaban kasa sun hadar da:
Nkeiruka Onyejeocha (APC Abia) - Kudirori 19
Nkem Abonta (Abia) - Kudirori 30
Ossai Nicholas Ossai (Delta) - Kudirori 29
Dachung Bagos (Plateau) - Kudirirrika 27
Simon Nwadkwom (Plateau) - Kudirori 22
Francis Uduyok (Akwa Ibom) - Kudirori 15
Gideon Gwani (Kaduna) - Kudirori 15
Femi Gbajabiamila (Lagos) - Kudirori 17

Asali: Facebook
Daga cikin kudirori 17 da Gbajabiamila ya kawo, tuni majalisar wakilai ta shigar da shida cikin doka, yayin da ragowar da suka hadar da yi wa kundin tsarin mulkin kasa kwaskwarima ke jiran sakamakon binciken kwamiti.
Haka kuma, daga cikin kudirori 59 da Honarabul Tajuddeen ya kawo zauren majalisar, 22 sun kasance na neman a samar da cibiyoyin Lafiya na Tarayya ne a wasu jihohi 21 da ke fadin kasar.
A wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, majalisar wakilai ta yi watsi da kudirin da ya nemi a rika dandake mutanen da aka kama da laifukan fyade a kasar nan.
KARANTA KUMA: Babu wata jiha a Najeriya da ta tsarkaka daga cutar korona - NCDC
Tun farko dai dan majalisar wakilai daga jihar Lagos, James Abiodun Faleke, shi ne ya gabatar da kudirin, inda ya nemi a rika dandake mutanen da aka kama sun aikata laifukan fyade.
Sai dai majalisar ta amince da a shimfida tsauraran hukunce-hukunce kan mutanen da aka kama da laifin fyade.
Majalisar ta cimma matsayar hakan ne yayin zaman da ta gudanar a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuni, bayan kiraye-kirayen da aka yi sakamakon yawaitar rahotannin fyade da ake samu a kasar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng