An yi Jina Jina da 'Yan Banga Suka Gwabza Kazamin Fada da 'Yan Bindiga

An yi Jina Jina da 'Yan Banga Suka Gwabza Kazamin Fada da 'Yan Bindiga

  • Rahotanni na nuni da cewa ‘yan bindiga sun kashe 'yan banga masu tsaron jama'a har 12 a kauyen Adabka da ke Bukkuyum, jihar Zamfara
  • Yayin da aka gwabza fadan, wasu da dama cikin 'yan bangan sun jikkata kuma tuni aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa
  • Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada cewa ba za su taɓa yin sulhu da ‘yan bindiga ba, ya ce za a cigaba da farautar su da yakar su

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kashe jami’an tsaron al’umma 12 a wani artabu da suka yi a kauyen Adabka da ke karamar hukumar Bukkuyum, Jihar Zamfara.

An bayyana cewa wasu da dama sun jikkata sakamakon harin, inda aka garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci.

Kara karanta wannan

'Dan bindiga ya tono sirrin 'yan ta'adda ga sojoji kafin 'yan uwasa su harbe shi

Yan bindiga
Yan bindiga sun kashe 'yan banga a Zamfara. Hoto: Zagazola Makama
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, duk da cewa ‘yan bindigar ma sun yi hasarar rayuka, ba a iya tantance adadin gawawwakin nasu ba domin sun kwashe su daga wurin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka gwabza fada da 'yan bindiga

Wani mazaunin Sabuwar Tunga, Malam Fahad, ya bayyana cewa harin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na safe ranar Laraba, inda ‘yan bindigar suka sace mutane da dama.

A cewarsa, yayin da maharan ke kokarin tserewa da wadanda suka sace, jami’an tsaron al’umma da ‘yan sa-kai daga wasu garuruwa suka yi kokarin tare su.

Daily Post ta wallafa cewa shaidar gani da idon ya ce:

“An kwashe kusan sa’a guda ana musayar wuta, har sai da ‘yan bindigar suka fara fama da karancin alburusai.
"Sai suka kira karin mayaka domin su taimaka musu. Daga nan sai suka mamaye jami’an tsaron al’umma, inda suka kashe 12 daga cikinsu kuma suka jikkata wasu.”

Kara karanta wannan

Kisan direbobi: Dattawan Arewa sun yi kaca-kaca da gwamnati da jami’an tsaro

Rundunar ‘yan sanda ba ta da labarin harin

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan Zamfara, Yazid Abubakar, ya ce bai da labarin harin da aka kai a Bukkiyum.

Wani tsohon jami’in soja da ke zaune a Dansadau ya alakanta karuwar hare-haren ‘yan bindiga da yarjejeniyar sulhu da aka yi da su a jihar Kaduna.

Ya ce irin wadannan yarjejeniyoyin sau da yawa kan kara musu karfin gwiwa wajen cigaba da kai hare-hare a wasu yankuna.

Gwamnan Zamfara zai cigaba da yaki

A bangarensa, Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya ce gwamnatinsa ba za ta taɓa yin sulhu da ‘yan bindiga ba.

Ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi bakuncin Shugaban Hafsan Sojin Sama, Hassan Bala Abubakar, wanda ya kai ziyarar ta’aziyya ga wadanda harin hadarin jirgin sama ya shafa.

Gwamna Dauda Lawal ya ce:

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Dalibar jami'a ta mutu a hannun yan bindiga duk da biyan miliyoyi a Zamfara

“Mun tsaya kan matsayar mu ta rashin sulhu da ‘yan bindiga, kuma sakamakon hakan yana bayyana. Zaman lafiya yana dawowa a Zamfara.”
Gwamnan Zamfara
Gwamnan Zamfara yayin wani taro. Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

An kama masu garkuwa a jihar Legas

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan sanda sun kama wasu mutane da ake zargi da garkuwa da mutane a jihar Legas.

Mutanen da aka kama 'yan kasar waje ne kuma sun yi amfani da jirgin sama ne wajen yaudarar wani mutum daga Kano zuwa Legas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel