Yadda Rufe Makarantu saboda Ramadan a Arewa Ya Jawo Hatsaniya da Martani
Wasu gwamnonin Arewacin Najeriya akalla hudu sun rufe makarantu saboda samun sauki a azumin watan Ramdan da ya jawo ce-ce-ku-ce a yankin.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - A yan kwanakin nan Arewacin Najeriya ta dauki zafi kan rufe makarantu da aka yi saboda azumin watan Ramadan.
Lamarin ya jawo maganganu daga bangarorin Musulmai da Kirista musamman a yankin har ma daga wasu bangaren Kudancin kasar.

Source: Twitter
Abin da ya jawo ce-ce-kuce a Arewacin Najeriya
A cikin wata sanarwa da Kungiyar CAN ta fitar a shafinta na Facebook, ta yi barazanar daukar matakin shari'a kan jihohin da suka rufe makarantun.
Wannan ya biyo bayan rufe makarantun da jihohin Kebbi da Kano da Katsina da kuma Bauchi suka yi saboda samun sauki a Ramadan.
A bagarensa, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya rufe makarantu har da na gaba da sakandare na tsawon makwanni biyar.
Amma dalilin haka, wasu iyaye sun yi korafi kan lamarin inda suke ganin hutun ya yi tsayi kuma zai shafi karatun yaransu.
Menene kungiyar CAN ta ce kan lamarin?
Kungiyar Kiristoci a Najeriya, CAN ta bukaci jihohin Kebbi da Bauchi da Katsina da Kano su janye matakin rufe makarantun.
Shugaban kungiyar, Daniel Okoh shi ya yi wannan roko inda ya ce matakin zai dakile ci gaban ilimi kuma take hakkin dalibai ne, cewar Punch.
Har ila yau, Kungiyar ta bukaci gwamnonin su tattauna da shugabannin addinai domin samar da mafita idan kuma ba haka ba za ta dauki matakin shari'a.

Source: Twitter
Gwamnonin Arewa 3 sun yi wa CAN martani
Sai dai gwamnonin jihohin nan da abin ya shafa sun yi zazzafan martani ga kungiyar CAN kan barazanarta.
Gwamnatin Kebbi ta ce ba za ta janye ba saboda kafin daukar matakin sai da ta tattauna da iyayen yara da shugabannin addinai.
A bangarenta, gwamnatin Kano ta bakin daraktan fadakarwa na ma'aikatar ilimi, Balarabe Kiru ya ce babu dalilin janye matakin saboda an yi da sanin masu ruwa da tsaki.
Har ila yau, kwamishinan ilimi a jihar Bauchi, Lawal Zayam ya tabbatar da cewa hutun Ramadan yana cikin tsarin zangon karatu na 2024/2025.
Martanin kungiyar dalibai a Najeriya
Kungiyar dalibai a Najeriya, NANS ta nuna takaici kan yadda aka dauki matakin rufe makarantun saboda azumin Ramadan.
Kungiyar daliban ta sha alwashin hawa kan tituna domin gudanar da zanga-zanga a Najeriya idan har ba a janye wannan mataki ba.
Jami'in hulda da jama'a na kungiyar, Samson Adeyemi ya ce sun ba gwamnatocin Kebbi da Kano da Katsina da kuma Bauchi wa'adi domin bude makarantun kafin daukar mataki.
Reno Omokri ya gargadi kungiyar CAN
Tsohon mai ba shugaban kasa shawara, Reno Omokri ya ce babu dalilin tayar da hankali kan batun rufe makarantu da wasu jihohin Arewa suka yi.
Omokri ya shawarci kungiyar CAN ta janye barazanar da ta yi, ya ce idan har dole sai ta yi magana kan lamarin akwai hanyoyin da suka dace.

Kara karanta wannan
"Ku bi a hankali," Omokri ya bukaci CAN ta guji shari’a da jihohi kan hutun Ramadan
Ya ce tsarin karatun Najeriya daidai yake da na Kiristanci a Birtaniya wanda Musulmai suke hakuri da shi a haka.

Source: Twitter
Ramadan: Sowore ya caccaki gwamnonin Arewa
Dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore ya soki gwamnonin Arewa kan rufe makarantu yayin Ramadan, yana mai cewa hakan jahilci da wawanci ne.
Sowore ya ce ko Saudiyya ba su rufe makarantu saboda azumi, yana cewa shugabannin Najeriya sun jahilci addini kuma ba su fahimci ilimi ba.
Sai dai wasu na ganin wadannan kalamai na Sowore sun yi tsauri duba da girman gwamnonin Arewa a cikin al'umma.

Source: Twitter
Ramadan: Jami'ar Maiduguri ta rage lokutan aiki
Mun ba ku labarin cewa hukumomi a jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno ta samar da sauki ga ma'aikatanta bayan rage lokutan aiki.
Rahotanni na nuni da cewa za a fara aiki daga karfe 8:00 na safe zuwa 3:00 na rana daga Litinin zuwa Alhamis, sai daga 8:00 zuwa 2:00 a ranar Jumu’a.
Hakan na zuwa yayin da ake ta ce-ce-ku-ce bayan wasu jihohin Arewacin Najeriya sun rufe makarantu saboda azumin watan Ramadan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

