Bayan An Yi Garkuwa da Shi, Wani Babban Malamin Addini Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Bayan An Yi Garkuwa da Shi, Wani Babban Malamin Addini Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • 'Yan bindiga sun hallaka babban limamin cocin katolika da suka yi garkuwa da shi ranar Talata 4 ga watan Maris, 2025 a yankin Kauru, Kaduna
  • Shugaban cocin katolika na Kafanchan, Rabaran Rabaran Jacob Shanet ya tabbatar da hakan yau Laraba, ya roƙi matasa su kwantar da hankalinsu
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Kaduna, Mansir Hassan ya ce sun tura dakaru yankin domin kamo waɗanda suka aikata kisan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Wani babban limamin cocin katolika a jihar Kaduna ya mutu a hannun ƴan bindiga bayan sun yi garkuwa da shi tun daren Talata, 4 ga watan Maris, 2025.

‘Yan bindiga sun kashe limamin cocin Saint Mary da ke garin Tachira a ƙaramar hukumar Kauru ta jihar Kaduna, Rabaran Fr. Sylvester Okechukwu.

Taswirar Kaduna.
Yan bindiga sun hallaka limamin coci bayan sun sace shi a Kaduna Hoto: Legit.ng
Source: Original

Shugaban cocin Kafanchan, Rabaran Fr. Jacob Shanet ne ya bayyana wannan labari mara daɗi a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi kira: Hatsabibin ɗan bindiga, Shekau ya mutu yayin arangama da ƴan ta'adda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun sace limamin katolika

Ya ce ƴan bindigar sun sace babban limamin ne daga gidansa da misalin karfe 9 na dare jiya, kuma daga bisani suka kashe shi a safiyar Laraba, 5 ga Maris, 2025.

Rabaran Fr. Shanet ya bayyana cewa har yanzu babu cikakken bayani kan dalilin da ya sa aka kashe Rabaran Okechukwu.

Sai dai ya ce mamacin ya kasance mutumin kirki da ke sadaukar da rayuwarsa don yada sakon zaman lafiya, soyayya da bege ga mabiyansa.

Katolika ta yi babban rashi a jihar Kaduna

Shugaban mabiya cocin ya ƙara da cewa mutuwar Rabaran din ta bar babban gibi a cikin Katolika, musamman a yankin Kafanchan.

"Ya kasance mai kokari, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidima ga Allah da al'umma. Mutuwarsa babban rashi ne ga kowa," in ji shi.

Shanet ya bukaci matasa da daukacin al’ummar yankin da su guji daukar doka a hannunsu, su ci gaba da zama cikin lumana da yin addu’a.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wuta kan masu taron siyasa a Najeriya, an harbi mutane 14

Rundunar ƴan sanda ta tura dakaru

Baya ga hakan, rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin.

Kakakin rundunar, Mansir Hassan, ya bayyana cewa an tura jami’an tsaro zuwa yankin da makwabtansa domin kamo wadanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.

Leadership ta tataro cewa an haifi marigayi Rabaran Fr. Sylvester Okechukwu a ranar 11 ga Disamba, 1980, kuma an nada shi babban limamin Cocin Katolika a ranar 11 ga Fabrairu, 2021.

Rabaran Sylvester Okechukwu.
Malamin cocin katolika ya mutu a hannun ƴan bindiga Hoto: Fr. Jacob Shanet
Source: Facebook

Wannan ba shi ne karon farko da ‘yan bindiga suka sace shi ba. A shekarar 2022, an taba sace shi daga Cocin St. Anthony’s da ke Fadan Kono a karamar hukumar Kauru.

Amma daga baya ƴan bindigar sun sake shi bayan ya shafe kwanaki uku a hannunsu a cikin jeji.

Ƴan bindiga sun sace limami a Edo

A wani labarin, kun ji cewa miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki cocin katolika da ke yankin ƙaramar hukumar Etsako ta Gabas a jihar Edo.

Kara karanta wannan

Yadda sufetan 'dan sanda da matasa suka lakadawa tsinannen duka ya rasu a Jos

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Edo ta tabbatar da afkuwar lamarin, tana mai cewa dakarunta sun kashe ɗaya daga cikin maharan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262