'Yan Sanda Sun Cafke Tsohon Jami'in Tsaro Mai Safarar Makamai ga 'Yan Bindiga
- Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen birnin tarayya Abuja ta samu nasara a ƙoƙarin da take yi wajen yaƙi da masu aikata laifuffuka
- Jami'an ƴan sandan sun cafke wani tsohon jami'in hukumar shige da ficen Najeriya (NIS), mai safarar makamai ga ƴan bindiga
- Ƴan sandan sun cafke wanda ake zargin ne ɗauke da manyan makamai lokacin da yake ƙoƙarin kai su ga ƴan bindiga a jejin Abuja-Kaduna
- Hakazalika, ƴan sandan sun cafke mutum 300 da ake zargi da aikata laifuffuka daban-daban tsakanin watan Janairu zuwa Maris 2025
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja ta cafke wani tsohon jami'in hukumar shige da ficen Najeriya (NIS).
Ƴan sandan sun cafke tsohon jami'in da ke ƙoƙarin sayar da makaman zamani ga ƴan bindiga da ke aiki a cikin dazukan hanyar Abuja-Kaduna.

Source: Facebook
Babban jami'in da ke kula da tawagar yaƙi da garkuwa da mutane, Mustafa Mohammed, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sanda sun yi ram da tsohon jami'in tsaro
Tsohon jami'in wanda ba a bayyana sunansa ba an kama shi ne bayan wani aikin bincike da ƴan sanda suka gudanar.
Mustafa Mohammed, ya ce aikin ya hana makaman daga isa hannun miyagu wadanda, a cewarsa, za su iya amfani da su wajen aikata mummunan laifi.
"Bayan samun bayanan sirri, hukumar ta cafke wadannan makaman daga hannun tsohon jami'in shige da fice da ke kokarin sayar da su ga ƴan bindiga da ke tada tarzoma a cikin dazukan Abuja-Kaduna."
"An samu bayanan sirrin a kan lokaci, kuma an cafke makaman a lokacin da yake kokarin kai su ga ƴan bindiga."
- Mustafa Mohammed
Mohammed ya ƙara da cewa, daga cikin makaman da aka ƙwato akwai wata bindiga ta zamani mai suna Scorpion CZ EVO3.
Ƴan sanda sun cafke miyagu a Abuja
A nasa ɓangaren, kwamishinan ƴan sandan birnin tarayya Abuja, Tunji Disu, ya bayyana cewa an kama mutum 300 a tsakanin watan Janairu da 28 ga Fabrairu, 2025.
"A ci gaba da ƙoƙarin kawar da laifi da ƴan bindiga a babban birnin tarayya Abuja, hukumar ƴan sanda ta ƙara yawan ayyukanta, inda ta gudanar da wasu manyan farmaki daga ranar 1 ga Janairu zuwa 28 ga Fabrairu, 2025."
"Waɗannan ayyukan sun sanya an cafke mutum 300 da ake zargi tare da ƙwato manyan makamai da haramtattun kayayyaki."
- Tunji Disu
Ƴan bindiga sun sace ɗan sanda a Abuja
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu tsagerun ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani babban jami'in ƴan sanda a babban birnin tarayya Abuja.
Ƴan bindigan sun sace ɗan sandan ne mai muƙamin CSP, Modestus Ojiebe wanda ya ke aiki a jihar Kwara, lokacin da yake tafiya a kan babbar hanyar zuwa Kubwa.
Jami'in ƴan sandan ya faɗa hannun ƴan bindigan ne lokacin da ya tsaya gyara motarsa sakamakon lalacewar da ta yi a kusa da barikin Dei-Dei.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


