Sunaye: CBN Ya Yi Sababbin Nade Nade, Mutum 16 Sun Samu Mukaman Darektoci
- Babban Bankin Kasa (CBN) ya yi sababbin nade-nade da zummar bunkasa yadda yake gudanar da ayyukansa kai tsaye
- Wata majiya daga bankin ta tabbatar da nada darektoci guda 16 da za su kula da bangarori daban-daban na bankin daga 3 ga watan Maris, 2025
- An yi nade-naden a bangaren kudi da kula da sauran bankuna, da kuma sassan da ke da alhakin sa ido kan sauran cibiyoyin kudi a fadin Najeriya
- Daga cikin wadanda su ka samu mukaman akwai Jide-Samuel Avbasowamen a matsayin darektan sashen fasahar bayanai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya nada sababbin darektoci 16 da za su jagoranci sassa masu muhimmanci daga ranar 3 ga Maris, 2025.
Wata majiya daga bankin ta ce an yi wadannan nade-nade ne domin karfafa ayyukansa, musamman a bangaren manufofi, doka da kuma kulawa da harkokin bankuna.

Asali: Twitter
The Cable ta wallafa cewa sababbin darektocin da aka nada sun hada da Jide-Samuel Avbasowamen a matsayin darektan sashen fasahar bayanai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai Abdullahi Hamisu, darektan sashen ayyukan banki; Ojumu Adenike, darektan sashen ayyukan lafiya; da Makinde Olanrewaju, shugaban sashen saye da samar da kayayyakin aiki.
CBN ta yi nade-nade a bangaren kudi
Jaridar the Nation ta ruwaito cewa a bangaren kudi, Babban bankin kasa ya nada Sike Ijeoma a matsayin darektan sashen manufofin kudi da dokoki.
Haka kuma, babban bankin ya nada Isa-Olatinwo Aisha a matsayin darekta a sashen kare hakkin masu amfani da bankuna; Oboh Victor Ugbem zai jagoranci sashen manufofin kudi.
Nakorji Musa zai shugabanci sashen kasuwanci da musayar kudi, yayin da Rakiya Yusuf za ta jagoranci sashen kula da tsarin biyan kudi.

Asali: Twitter
Sai kuma Vincent Modesola da bankin ya nada a matsayin wanda zai jagoranci sashen tsare-tsare da kirkire-kirkire.
Farouk Muhammad zai shugabanci sashen kula da ajiyar kudaden kasa, yayin da Akinwunmi Olubukola Akinniyi zai jagoranci sashen kula da harkokin bankuna.
Sauran nade-naden da CBN ya yi
Baya ga haka, Solaja Mohammed-Jamiu zai jagoranci sashen kula da sauran cibiyoyin kudi, Hassan Umar zai shugabanci sashen kula da cibiyoyin raya tattalin arziki da hada-hadar kudi.
Adedeji Adetona zai jagoranci sashen kula da kudade da gudanar da rassan bankin, yayin da Okpanachi Moses zai shugabanci sashen kididdiga.
CBN: Mun ceto tattalin arzikin Najeriya
A baya, kun samu labarin cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa matakan da ya dauka sun hana hauhawar farashin kaya wuce 42.81% a watan Disamba na shekarar 2024.
A cewar CBN, daya daga cikin muhimman sauye-sauyen da aka aiwatar shi ne karfafa tsare-tsaren kudi domin dakile hauhawar farashin kayayyaki da bunkasa tattalin arziki.
Haka nan, babban bankin ya yi hasashen cewa kudaden da ‘yan Najeriya ke aikowa daga kasashen waje zai kai Naira tiriliyan 31.79 idan aka kammala kididdigar zangon karshe na 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng