'Mun Daina Ɗaukar Ɗawainiyarku': Jihohi na Fuskantar Barazana daga Gwamnatin Tinubu

'Mun Daina Ɗaukar Ɗawainiyarku': Jihohi na Fuskantar Barazana daga Gwamnatin Tinubu

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba za ta iya ci gaba da daukar dawainiyar biyan bashin da gwamnatocin jihohi suka kasa biya ba
  • Akanta Janar ta tarayya ta bukaci jihohi su dakile asarar kudaden shiga, su kara samun kudade don rage dogaro da gwamnatin tarayya
  • Dakta Sakirat Madein ta ce za a zamanantar da harkokin biyan albashi tare da bukatar ma'aikata su koyi amfani da fasahohin zamani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba za ta kara daukar dawainiyar biyan bashin da gwamnatocin jihohi suka kasa biya ba.

Akanta Janar ta tarayya, Dakta Oluwatoyin Sakirat Madein, ta bukaci jihohi da su dakile barna a hanyoyin kudaden shiga domin bunkasa tattalin arzikinsu.

Gwamnatin tarayya ta gargadi jihohi kan basussukan da suke ciyowa su gaza biya
Gwamnatin tarayya ta daina biyan basussukan da jihohi suka karbo, suka gaza biya. Hoto: @NGFSecretariat
Asali: Twitter

Gwamnati za ta daina biyawa jihohi bashi

Kara karanta wannan

Tinubu zai rabawa jihohin Najeriya Naira tiriliyan 1, an fadi ayyukan da za su yi

Jaridar The Nation ta rahoto Dakta Sakirat Madein tana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wannan mataki zai tabbatar da cewa jihohi na samun kudaden shiga a kan kari, kuma ba za a cusa wa Gwamnatin Tarayya daukar dawainiyar biyan bashi ba."

Ta bayyana hakan ne yayin wata ziyarar aiki a ofishin biyan albashi na tarayya da ke Kano, kamar yadda wata sanarwa daga ofishin Akanta Janar na tarayya (OAGF) ta tabbatar.

Sanarwar, wacce daraktan yada labarai da hulda da jama’a, Bawa Mokwa, ya fitar, ta nuna bukatar kiyaye tsare-tsaren kula da kudade na gwamnatin tarayya.

Gwamnati za ta zamanantar da biyan albashi

Dakta Sakirat Madein ta bukaci jami’an ofisoshin biyan albashi da su tabbatar da bin ka’idojin inganta harkokin kudi da gwamnati ke aiwatarwa.

Ta kuma jaddada bukatar barin tsofaffin hanyoyin sarrafa kudi, tana mai cewa yanzu ana bukatar amfani da fasahar zamani wajen gudanar da ayyukan lissafin kudi.

Kara karanta wannan

Soyayya ta ƙare: Wani ɗan Najeriya ya lakaɗawa budurwarsa dukan tsiya har ta mutu

"Gwamnati za ta kawar da hanyoyin aikin kudi na hannu. Fasaha ce mafita a bangaren lissafin kudi," inji Akanta Janar din.

Akanta Janar din ta bayyana cewa ofishinta ya fara aiwatar da tsarin gudanar da ayyuka na zamani don zamantantar da duka harkokin kudi, ciki har da na ofisoshin biyan albashi.

An nemi ma'aikata su koyi sarrafa kwamfuta

Akanta Janar ta tarayya ta aika sako ga jihohi kan biyan basussukan da suka gagara biya
Akanta Janar ta tarayya, Dakta Madein ta ce za a zamantar da biyan albashi. Hoto: @FMINONigeria
Asali: Twitter

Ta kuma bukaci jami’an ofishin da su rungumi tsarin kimanta aiki na zamani wanda zai maye gurbin tsohon tsarin APER.

Wannan tsari zai kunshi duka ma’aikata, kuma zai zama hanyar auna nasarar shugabanci, a cewarta, inji rahoton Punch.

Ta yi kira ga jami’an ofisoshin biyan albashi da su kasance cikin shirin amfani da fasahohin zamani a ayyukansu tare da kwarewa a kan na’urorin kwamfuta.

A madadin jami’an yankin Arewa maso Yamma, shugaban kwamitin ofisoshin biyan albashi, Aminu Umar, ya gode wa Akanta Janar bisa wannan ziyara.

Kara karanta wannan

Bayan saukar abinci, gwamnatin Tinubu za ta karya farashin kayan gini

Aminu Umar ya bayyana ziyarar a matsayin 'yar manuniya ga duk wanda zai gaji kujerar Dakta Sakirat Madein a nan gaba.

'Jihohin Najeriya sun rage karbo bashi' - DMO

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ofishin kula da basussuka (DMO) ya ce jihohi sun rage basussukan cikin gida da Naira Tiriliyan 1.79 cikin watanni uku.

Alkaluman sun bayyana cewa jihohin Arewa maso Gabas sun fi rage basussuka da kashi 95%, wanda ya kai Naira Biliyan 40.69 daga Janairu zuwa Maris.

Duk da wannan ragi, jimillar rancen da Najeriya ta karbo ya karu da kusan Naira Tiriliyan 24, wanda ya hada da na jihohi da Gwamnatin Tarayya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel