Tinubu Zai Rabawa Jihohin Najeriya Naira Tiriliyan 1, An Fadi Ayyukan da Za Su Yi

Tinubu Zai Rabawa Jihohin Najeriya Naira Tiriliyan 1, An Fadi Ayyukan da Za Su Yi

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince a rabawa jihohi N1trn domin bunkasa kiwon lafiya, daukar ma’aikata, da inganta asibitocin PHC
  • Ministan lafiya ya ce gwamnati na shirin horar da fiye da ma’aikatan lafiya 60,000 tare da bunkasa kiwon lafiyar mata da jarirai
  • Gwamnati na kokarin rage mace-macen mata yayin haihuwa, samar da magani kyauta, da shawo kan cututtuka kamar shan inna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da wani shiri na bada kudi har Naira tiriliyan 1 ga jihohin Najeriya.

An ce za a yi amfani da kudin wajen inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (PHC), daukar ma’aikatan lafiya, da bunkasa ayyukan lafiya a jihohin.

Gwamnatin tarayya ta yi zama da kwamitin sarakunan Arewa kan kiwon lafiya
Tinubu ya amince a rabawa jihohi Naira tiriliyan 1 domin inganta kiwon lafiya. Hoto: @officialSKSM
Asali: Twitter

Ministan lafiya ya bayyana hakan a taron bitar zangon farko na shekarar 2025 na kwamitin sarakunan Arewa kan inganta kiwon lafiya (NTLC) a Abuja, inji rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Ramadan: Hanyoyi 8 da Musulmi zai kasance cikin koshin lafiya a watan azumi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin rage mutuwar mata da jarirai

Farfesa Mohammad Ali Pate, ya ce wannan matakin, tare da karin kasafin kudin lafiya a duk shekara, na nuna kudirin gwamnati na habaka tsarin kiwon lafiya a kasar.

Ministan ya bayyana cewa gwamnati na kokarin karfafa cibiyoyin kiwon lafiya ta hanyar horar da fiye da ma’aikatan lafiya 60,000.

Hakanan, gwamnati za ta fadada shirin farfado da dakunan shan magani a jihohi, da kuma inganta kiwon lafiyar mata masu juna biyu da jarirai.

Ya kara da cewa shirin rage mutuwar mata masu juna biyu da jarirai karkashin tsare-tsaren Renewed Hope Agenda na shugaba Tinubu zai mayar da hankali kan rage mace-macen mata yayin haihuwa.

Sannan shirin zai samar da magani kyauta ga mata masu matsalolin haihuwa, da kuma cire cikas na kudade ga matan, musamman a yankunan karkara.

Ministan ya jaddada muhimmancin shayar da nono zalla da amfani da abinci mai gina jiki ga yara domin tabbatar da lafiyar su.

Kara karanta wannan

Gwamnan Sakkwato ya waiwayi malaman musulunci, an yi masu tanadin Ramadan

Barazanar cutar Polio da tasirin NTLC

Ministan lafiya, Farfesa Pate ya yi magana kan tasirin kwamitin sarakunan Arewa na kiwon lafiya
Ministan lafiya, Farfesa Pate ya bayyana shirin gwamnatin Tinubu na inganta kiwon lafiya. Hoto: @muhammadpate
Asali: Twitter

Farfesa Ali Pate ya bayyana cewa bullar nau’in cutar shan inna (Type 2 - cVPV2) na ci gaba da zama barazana ga lafiya a Najeriya.

“Wannan ba sabuwar matsala ba ce. Mun taba fuskantar irin wannan a baya, amma tare da kwazon shugabanni, jajircewa, da hadin gwiwar al’umma, mun samu nasarar shawo kanta,” inji Farfesa Pate.

Ya yabawa rawar da sarakuna ke takawa wajen wayar da kan jama’a da karfafa yaki da cututtuka, yana mai cewa gudunmawar su na da matukar muhimmanci wajen dorewar nasarorin da aka samu a kiwon lafiya.

Ministan ya ce kwamitin NTLC yana daya daga cikin shirye-shiryen sa-kai mafi dadewa a duniya, wanda ya kasance yana aiki tsawon shekaru 16 ba tare da katsewa ba.

Ya kara da cewa makonni da suka gabata, ya jagoranci wata ziyara zuwa jihohi hudu tare da shugaban hukumar kula da yaki da cutar shan inna ta Duniya (POB) da shugaban NTLC.

Kara karanta wannan

Ana zargin yana tsakiyar fada da El Rufai, Uba Sani ya samu mukami a gwamnatin Tinubu

A lokacin ziyarar, sun gano wasu matsaloli masu matukar bukatar a magance su domin ci gaba da inganta kiwon lafiya a kasa.

Tinubu ya ware N4.5bn domin yakar kanjamau

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta amince da Naira biliyan 4.5 domin sayen magungunan kanjamau don tallafa wa masu dauke da cutar.

Ministan Lafiya, Ali Pate, ya bayyana cewa shirin zai tabbatar da wadatar magani ga masu cutar ba tare da tangarda ba, bayan janye tallafin gwamnatin Amurka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel