Alfanu da falalar shayar da jarirai nonon uwa zalla ga jikin jariran

Alfanu da falalar shayar da jarirai nonon uwa zalla ga jikin jariran

- An kara tabbatar da binciken cewa jarirai basu bukatar ruwa ko abinci a watannin farko 6

- Nonon uwa na samarwa da jarirai garkuwa daga kwayoyin cutuka na farko da kan kawo wa yara hari

- Sannu a hankali iyaye na kara wayewa kan iya kula da yaransu

A farkon watan Agusta ne dai ake bikin shayarwar jarirai da nonon uwa, kuma na bana ya sami tagomashi a fadin Najeriya. Legit.ng ta bi muku kadin bikin na babban asibitin Abuja, inda aka yi bitar wayar wa da iyaye mata kai kan shayarwa da nono zalla ba mis.

Alfanu da falalar shayar da jarirai nonon uwa zalla ga jikin jariran
Alfanu da falalar shayar da jarirai nonon uwa zalla ga jikin jariran

Hajiya Mariya Mukhtar Yola ce ta shugabanci shirin a asibitin, inda dama itace shugabar bangaren likitanci ga yara da jarirai ta asibitin. Ms. Mariya Yola, ta yi kira ga iyaye da su guji baiwa yara ruwa ko abinci a watanni shida na farkon haihuwa domin yaran basu bukatar su.

A cewarta dai, magani kawai yaran ke bukata idan an basu a asibiti, amma banda kari, sai nono zalla. Kiranta ya kara wayarwa da iyaye kai kan alfanun shayar da nono, wanda ya hada da kara wa yaran karfin garkuwar jiki don yaki da cutuka, sannan da samar wa da yaran ababen da jiki ke bukata don habaka.

DUBA WANNAN: Malami ya caccaki Magu kan yaki da rashawar gwamnati

Da yawa a kasashen mu daai iyaye sukan karyata wannan bincike, su ce wai ai jariri dole ya sha ruwa, kuma kin bashi wai zalunci ne, basu dai sani ba, a cikin nonon uwa, akwai ruwa hade da abinci, saboda haka, cika wa yaro ciki da ruwa yana tokare yawan kayan amfanin da yaro zai tsotsa a mama, domin da ya ara sai ya koshi.

Bincike kuma ya tabbatar da cewa, lallai nonon farko da uwa ke fitarwa, bayan ta haihu, yaffi komai amfani ga dukkan jikin jariri a rayuwarsa, don haka, matse shi a zubar rashin sani ne, a baiwa yaro ya sha.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: