Da duminsa: Sabon nau'in cutar Shan Inna ta kama mutum 395 a jihohi 27 na Najeriya da FCT

Da duminsa: Sabon nau'in cutar Shan Inna ta kama mutum 395 a jihohi 27 na Najeriya da FCT

  • Sabuwar nau'in cutar shan Inna ta barke a Najeriya inda ta kama yara 395 a jihohin kasar nan 27 da babban birnin tarayya na Abuja
  • Kamar yadda daraktan hukumar NPHCDA, Dr Faisal Shuaib ya sanar, ya ce babu gaskiya a zantukan masu cewa tsohuwar cutar shan inna ce ta dawo
  • Dr Faisal ya ce sabuwar cutar ta bayyana ne sakamakon gibin da ake samu na garkuwar jikin kananan yara da kuma rashin zuwa riga-kafi

Najeriya ta na fuskantar barkewar sabon nau'in cutar shan inna mai suna Circulating Nigeria Mutant Poliovirus Type 2 (cMPV2) a jihohi 27 na kasar da babban birnin tarayya da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Daraktan National Primary Healthcare Development Agency (NPHCDA), Dr Faisal Shuaib, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis yayin martani ga rahotannin kafafen yada labarai na cewa sabon nau'in cutar shan Inna ya barke a wasu jihohi.

Kara karanta wannan

Burin Tinubu ya gamu da cikas na farko, Shugaban Yarbawan Afenifere ya ki mara masa baya

Da duminsa: Sabon nau'in cutar Shan Inna ta kama mutum 395 a jihohi 27 na Najeriya da FCT
Da duminsa: Sabon nau'in cutar Shan Inna ta kama mutum 395 a jihohi 27 na Najeriya da FCT. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa, cibiyar ta ce akasin yadda rahotanni ke yawo, ba a samu wani wanda Wild Polio Virus (WPV) ta kama ba a kasar nan tun shekarar 2016.

“An tabbatar da cewa Najeriya da Afrika baki daya ta fita daga kangin cutar Wild Polio Virus (WPV) a 2020 tun bayan tsananin tantancewa da cibiyar yaki da cutar shan inna ta Afrika ta yi, wanda ya dauke ta shekaru 3 amma bata samu ko burbushin cutar ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Har a yau, ba a sake samun cutar WPV a ko ina na kasar nan," takardar tace.

Ya yi bayanin cewa, sabuwar nau'in cutar shan inna da ta bayyana ta samo asali ne da rashin garkuwar jiki mai karfi a kananan yara da sauran dalilai da suka hada da, yin rigakafi da kuma rashin zuwa taron gangamin wayar da kai yayin riga-kafi.

Kara karanta wannan

FG ta bayyana sharudda 5 da ta gindaya wa Twitter kafin dage dokar haramci

Omicron: Abin da ya dace a sani kan sabon samfurin COVID-19 da ke neman sake rufe kasashe

A wani labari na daban, The Cable tace hukumar lafiya ta Duniya ta sa wa wannan samfuri suna da Omicron, kuma ta tabbatar da hadarin cutar saboda irin yadda ta ke yawan hayayyafa.

Omircon ta na rikida har nau’i 32 a jikin Bil Adama, hakan ya nuna ta fi irinsu samfurin Delta ikon rikida, Masana sun ce wannan zai jawo ta gagara jin magani da wuri.

An tabbatar da cewa nau’in cutar B.1.1.529 ya fi samufurin Delta sauran yaduwa a tsakanin mutane. Masana kiwon lafiya ba su iya tabbatar da inda cutar ta fito ba. Abin da aka sani shi ne an fara ganin mai dauke da samufurin ne a ranar 23 ga watan Nuwamba, 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel