Mutanen Gari Sun Firgita da Cewa 'Allah Ya Yi Wahayi' Makiyaya za Su Kai Hari
- Rundunar ‘yan sanda a jihar Imo ta kama wani mutum da ake zargi da yada saƙon barazana ga mazauna yankin Irete
- Wanda ake zargin ya bayyana cewa ya fitar da saƙon ne bisa umarnin wata malamar addini da ta ce an mata wahayi
- ‘Yan sanda sun gargadi jama’a kan yada labaran karya da ke haddasa fargaba da hargitsi a cikin al’ummar jihar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Imo - Rundunar ‘yan sanda a jihar Imo ta kama wani mutum mai suna Chidi Azonibe, mai shekara 35, bisa zargin yada saƙon barazana da ya haddasa fargaba a yankin Umuoba da ke Irete.
Kakakin rundunar ‘yan sanan jihar, DSP Henry Okoye, ya ce wanda ake zargi ya amsa cewa shi ne ya raba takardun barazanar tare da ɗan uwansa bisa umarnin wata malama mai suna Ijeoma.

Kara karanta wannan
Ana zargin akwai lauje cikin naɗi da aka kama jami'in NIS ɗauke da manyan makamai

Asali: Facebook
Punch ta wallafa cewa an gano takardun ne a daren Litinin, 10 ga watan Fabrairu, a kofar gidaje da dama a yankin Irete, inda suka haddasa tsoro da tashin hankali a tsakanin mazauna yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka gano saƙon barazanar hari a Imo
Takardar barazanar da aka watsa a yankin Irete ta bayyana cewa:
"Mu ne Fulani makiyaya! Muna daf da kawo muku hari! Ku saurare mu"
An ruwaito cewa saƙon ya jefa mutane cikin firgici, inda wasu suka fara fargabar hari daga makiyaya.
Wanda ake zargin, Chidi Azonibe, ya bayyana cewa an rubuta saƙon barazanar ne da umarnin wata malamar addini mai suna Ijeoma daga cocin Assembly, Irete.
A cewarsa, malamar addinin ta shaida masa cewa ta sami wahayi daga Allah cewa makiyaya za su kai hari.
A karkashin haka ne ta bukaci shi da ɗan uwansa, Amanea, su yada saƙon a tsakanin al’umma don su kasance cikin shiri.
Matakin da 'yan sanda suka dauka
A cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Imo ta fitar, DSP Henry Okoye ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin bayan binciken da suka gudanar domin gano asalin saƙon barazanar.
Kakakin 'yan sandan ya ce:
“Mun kama Chidi Azonibe, wanda ya amsa cewa shi da ɗan uwansa sun yada wannan saƙo bisa umarnin malamar cocinsu, Rabaran Ijeoma.
An fara kokarin kama sauran masu hannu a wannan lamari, ciki har da malamar addinin da ake zargi da umartar su.”
Haka kuma, ‘yan sanda sun tabbatar da cewa saƙon ya haddasa fargaba sosai a tsakanin mazauna yankin Irete da Owerri, inda jama’a suka shiga cikin rudani da firgici.
'Yan sandan Imo sun yi gargadi
DSP Henry Okoye ya bayyana cewa wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a kansa.
Ya kuma yi gargaɗi cewa duk wanda aka kama yana yada labaran ƙarya ko masu tayar da hankali zai fuskanci hukunci mai tsanani.
Sojoji sun fatattaki 'yan fashi a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun rundunar sojin Najeriya sun fatattaki wasu 'yan fashi da makami a jihar Kaduna.
Sojojin Najeriya sun samu kiran gaggawa a lokacin da 'yan fashin suka tare hanya wanda daga nan suka tunkare su suka fatattake su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng