Majalisa Ta Amince: Gwamnatin Tinubu Za Ta Kashe Naira Tiriliyan 54.99 a 2025

Majalisa Ta Amince: Gwamnatin Tinubu Za Ta Kashe Naira Tiriliyan 54.99 a 2025

  • Majalisar wakilai ta amince da kasafin 2025 na Naira tiriliyan 54.99 domin raya ƙasa, biyan basussuka da inganta tattalin arziki
  • An ware Naira tiriliyan 23.963 domin manyan ayyuka, yayin da aka ware Naira tiriliyan 14.317 don biyan basussuka da nauyin kuɗi
  • Shugaba Bola Tinubu ya ce an samu ƙarin kuɗin shiga a FIRS, Kwastam da hukumomi, wanda ya sa kasafin ya kai N54.99trn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar wakilai ta amince da kasafin 2025 na Naira tiriliyan 54.99, wanda ya mayar da hankali kan ayyukan raya ƙasa da ci gaban tattalin arziƙi.

Gwamnati ta bayyana cewa wannan kasafin kuɗi zai taimaka wajen cika muhimman buƙatun tattalin arziki da ayyukan ci gaba na ƙasa.

Majalisar wakilai ta amince da kasafin 2025 da Tinubu ya gabatar mata na N54.99trn
Gwamnatin Tinubu za ta kashe N54.99trn na kasafi a 2025 bayan amincewar majalisar wakilai. Hoto: @officialABAT, @HouseNGR
Asali: Twitter

Majalisa ta amince da N54.99trn a kasafin 2025

Kara karanta wannan

"A yafe mana," Kamfanin MTN ya ba da haƙuri kan karin farashin 'data'

An ware Naira tiriliyan 3.645 don tallafin dokoki, da Naira tiriliyan 14.317 don biyan basussuka da sauran nauyin kuɗi na gwamnati, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ware Naira tiriliyan 13.64 don ayyukan yau da kullum, wanda ya haɗa da albashi da kuɗin gudanarwa, sai kuma Naira tiriliyan 23.963 da aka ware don manyan ayyuka.

Kasafin shekarar 2025 ya nunka na shekarun baya, domin tabbatar da ci gaban tattalin arziki da inganta ayyukan jama’a.

Tasirin kasafin 2025 ga cigaban Najeriya

Ana sa ran za a mayar da hankali kan gina tituna, asibitoci, da manyan tsare-tsaren ci gaba waɗanda za su haɓaka tattalin arzikin Najeriya.

Majalisar ta bayyana cewa, haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da majalisa zai taka rawa wajen tabbatar da nasarar wannan kasafin kuɗi.

Channels TV ta rahoto cewa kasafin 2025 zai taimaka wajen inganta ayyukan gwamnati da tabbatar da daidaito a harkokin kuɗi a sabuwar shekarar kasafin.

Kara karanta wannan

Ta faru ts kare: Kamfanin MTN ya kara kudin data, ya saki sabon farashi

Tinubu ya kara kasafin 2025 zuwa N54.00trn

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaban kasa Bola Tinubu gabatarwa majalisar tarayya da bukatar amincewa da ƙarin kasafin 2025 daga N49.7trn zuwa N54.99trn.

Tinubu ya ce ya kara kudin ne sakamkon karin kuɗaden shiga da aka samu a wasu hukumomin gwamnati ciki har da N1.4trn daga FIRS, da N1.2trn daga kwastam.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel