Tsare Tsaren Shari’a da na Siyasa da Ake bi wajen Kirkiro Sababbin Jihohi a Najeriya
- Majalisar wakilai ta karɓi bukatun ƙirƙirar sababbin jihohi 31 yayin da ake duba gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999
- Don yin gyaran kundin tsarin mulki, ana buƙatar goyon bayan kashi biyu bisa uku na 'yan majalisa da majalisun dokoki 24 na jihohi
- Ana buƙatar cikakken bin sharuddan da aka gindaya a sashe na 8(1) na kundin tsarin mulki don ƙirƙirar sabuwar jiha a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - A zaman majalisar wakilai na ranar Alhamis 6 ga watan Janairun 2025, mataimakin kakakinta, Benjamin Kalu, ya ce an gabatar da bukatu na ƙirƙirar sabbin jihohi 31
Majalisar dokoki ta 10 tana duba yiwuwar gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, wanda ya haɗa da bukatar ƙirƙirar sabbin jihohi a ƙasar.

Asali: Facebook
Yadda tsare-tsaren gyara kundin tsarin mulki suke
Gyaran kundin tsarin mulki na nufin gyara ko ƙara wani abu a rubutaccen tsarin mulkin ƙasa domin ya dace da bukatun al'umma, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi hanyar gyara idan an ga akwai buƙata, hanya da ake bi don yin wannan gyaran na danganta da sashen da ake son gyara.
Yawancin gyaran da ake yi yana buƙatar goyon bayan kashi biyu bisa uku na ‘yan majalisar dattawa da na wakilai tare da goyon bayan majalisun dokoki 24 na jihohi.
Ka'idojin da ake bi domin kirkirar sabuwar jiha
Sassan da suka shafi ƙirƙirar sabuwar jiha, ƙaramar hukuma, ko gyaran iyakokin jihohi suna buƙatar cika wasu ƙarin sharudda.
Don gyaran kundin tsarin mulki, ana gabatar da kudirin gyara a majalisar dokoki kuma dole ne ya samu amincewar 'yan majalisa, Voice of Nigeria ta ruwaito.
Bayan gabatar da kudirin, ana karanta shi karo na farko, sannan a tattauna a kan ma'anarsa kafin a tura shi kwamitin gyara kundin tsarin mulki.
Kwamitin zai gudanar da taron sauraran ra’ayoyin jama’a kafin yanke shawara kan gyaran da za a amince da shi ko watsi da shi.
Daga nan sai a dawo da rahoton ga majalisa inda za a kada kuri’a kan kowane bangare na kudirin gyara kundin tsarin mulkin.
Yawan adadin kuri'un da ake bukata a Majalisa
A kowane zauren majalisa (dattawa da wakilai), ana amfani da kaɗa kuri’a a zamanance domin tabbatar da cewa an kai yawan adadin da ake bukata.
Wannan yana tabbatar da cewa yawan 'yan majalisar da suka halarta bai gaza adadin kashi biyu bisa uku da ake bukata ba.
Idan an sami goyon bayan kashi biyu bisa uku daga majalisun dokoki na jihohi 24, sai a mayar da kudirin zuwa ga majalisar tarayya.
Daga nan sai a tura kudirin ga shugaban ƙasa domin ya sanya hannu, wanda zai zama doka idan ya amince da shi, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan
'Dan Majalisa ya fito ya faɗi gaskiya, ya bayyana kuɗin da aka tura wa ƴan bindiga
Domin ƙirƙirar sabuwar jiha, ana buƙatar bin tsauraran sharudda da aka shimfiɗa a cikin sashe na 8(1) na kundin tsarin mulki.
Kirkirar jiha: Rawar da yan majalisa za su taka
Dole ne a sami bukatar ƙirƙirar jiha daga kashi biyu bisa uku na wakilan yankin a majalisar dattawa, wakilai, da ƙananan hukumomi.
Bayan haka, ana gudanar da zaɓen raba gardama a yankin da ake son ƙirƙirar jiha, wanda dole ne ya samu goyon bayan kashi biyu bisa uku.
Sakamakon zaɓen raba gardama dole ne ya samu amincewar mafi rinjayen majalisun dokoki na jihohin Najeriya.
Daga nan sai a koma majalisar tarayya, sannan su kada kuri’a da kashi biyu bisa uku na ‘yan majalisar tarayya na dattawa da wakilai.
Tun dawowar mulkin dimukraɗiyya a 1999, ba a ƙirƙiri wata sabuwar jiha ba a Najeriya, duk da yawan shawarwarin da aka gabatar.
Martanin majalisa kan ƙirƙirar sababbin jihohi
Kun ji cewa Majalisar Wakilai ta bayyana cewa ba ta gabatar da kudirin kafa sababbin jihohi 31 ba, ta ce rahotannin da ke yawo kan hakan ba su da inganci.

Kara karanta wannan
Ba a gama da ƙudirin haraji ba, Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon ƙarin harajin NPA
Mataimakin Kakakin Majalisa, Benjamin Kalu ya ce an karɓi ƙudirin kafa jihohi 31, ya ce wannan ƙudiri ba matsaya ba ce ta majalisar baki ɗaya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng