'Yan Bindiga Sun Yi Barna a Gombe, Sun Hallaka Malamin Addini
- An shiga jimami a Gombe bayan wasu ƴan fashi da makami sun hallaka wani malamin addinin Kirista mai suna Rabaran Bala Galadima
- Ƴan fashi da makamin sun hallaka malamin addinin Kiristan ne a gidansa da ke garin Lubo cikin ƙaramar hukumar Yamaltu-Deba
- Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya yi alhini kan kisan, aka ji ya buƙaci jami'an tsaro da su farauto waɗanda suka yi aika-aikan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Gombe - Wasu ƴan bindiga da ake zaton ƴan fashi da makami ne sun hallaka wani malamin addinin Kirista, Rabaran Bala Galadima a jihar Gombe.
Ƴan bindigan sun kashe malamin ne a garin Lubo, cikin ƙaramar hukumar Yamaltu-Deba ta jihar Gombe a daren ranar Lahadi.

Source: Facebook
Ƴan fashi sun kashe malamin Kirista a Gombe
Jaridar Leadership ta ce Rabaran Bala Galadima shi ne babban mai wa’azi a cocin Evangelical Church Winning All (ECWA) da ke garin Lubo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sannan rahoton jaridar The Punch ya bayyana cewa ƴan fashi da makamin sun kashe shi ne a cikin gidansa da sanyin safiyar Litinin.
Hukumar ƴan sanda ta tabbatar da lamarin
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin.
"Abin takaici ne, duba da yadda aka harbe shi a bayansa, alamu sun nuna ya yi ƙoƙarin tserewa ne, wanda hakan abu ne da ya saba faruwa a irin wannan yanayi."
- DSP Buhari Abdullahi
Gwamnan Gombe ya yi Allah-wadai da kisan
Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan kisan gilla da aka yi wa limamin cocin, inda ya ba da umarnin a kamo masu laifin.
A wata sanarwa da hadiminsa, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar a shafinsa na Facebook, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana matuƙar bakin cikinsa kan kisan gillar da aka yi wa malamin addinin Kiristan.
"Gwamna Inuwa Yahaya ya yi tir da wannan ɗanyen aiki, yana mai bayyana shi a matsayin harin da ya ke barazana ga zaman lafiya da tsaron da aka daɗe ana morewa a jihar Gombe."
"Gwamnan ya jaddada cewa ba za a lamunci irin wadannan munanan ayyuka da ka iya kawo naƙasu ga zaman lafiyar al’umma ba."
- Ismaila Uba Misilli
Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, cocin ECWA, da kuma ɗaukacin al’ummar Kirista.
Ya kuma yi addu’a Allah ya ji ƙansa ya ba iyalansa da makusantansa hakurin jure wannan rashi.
Ƴan bindiga sun kai hari a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Rabbah ta jihar Sokoto.
Miyagun ƴan bindigan a yayin harin da suka kai da tsakar dare sun yi ta harbe-harbe wanda hakan ya yi sanadiyyar rasuwar mutum ɗaya tare da raunata wani mutum ɗaya.
Ƴan bindigan sun kuma tattara mutane masu yawa sun tafi da su zuwa cikin daji da ƙarfin tsiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

