'Yan Sanda Sun Nuna Kwarewa, Sun Yi Ajalin Tantiran 'Yan Bindiga

'Yan Sanda Sun Nuna Kwarewa, Sun Yi Ajalin Tantiran 'Yan Bindiga

  • Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta gayawa duniya nasarorin da ta samu kan ƴan bindiga da masu aikata laifuffuka a jihar
  • Kakakin rundunar ƴan sandan ya bayyana cewa an hallaka ƴan bindiga 11 tare da ceto mutane 85 da aka yi garkuwa da su a Janairun 2025
  • DSP Abubakar Sadiq-Aliyu ya ƙara da cewa jami'an rundunar sun ƙwato dabbobi masu yawa da ƴan bindiga suka sace a fadin jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta bayyana nasarorin da ta samu kan ƴan bindiga da sauran masu aikata laifuka a cikin watan Janairun 2025.

Rundunar ƴan sandan ta ce ta samu nasarar kashe ƴan bindiga 11 tare da ceto mutum 85 da aka sace a cikin watan Janairu.

'Yan sanda sun hallaka 'yan bindiga a Katsina
'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga 11 a Katsina Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ne ya bayyana hakan a shafin X a ranar Asabar, 8 ga watan Fabrairun 2025.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun yi taron dangi kan 'yan ta'adda, sun hallaka miyagu masu yawa

Ƴan sanda sun kama miyagu a jihar Katsina

Kakakin rundunar ya ce ƴan sanda sun kuma ƙwato dabbobi 213 da aka sace a faɗin jihar.

Kamar yada sanarwa ta bayyana, a cewarsa, rundunar ta kama mutane 45 da ake zargi da aikata manyan laifuffuka guda 52.

Daga cikin waɗanda aka kama akwai, mutum huɗu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, mutum shida da ake zargin sun aikata laifin kisan kai.

Sauran sun haɗa da, mutum bakwai da ake zargin ƴan fashi da makami ne da mutum uku da ake zargin suna bayar da bayanai ga ƴan bindiga.

DSP Sadiq Aliyu ya ƙara da cewa sauran mutum 32 an kama su ne kan zargin aikata wasu laifuka daban-daban.

Laifuffukan da ake zarginsu da aikatawa sun haɗa da fashi da makami, kisan kai, garkuwa da mutane da fyade, da sauransu.

An ƙwato kayayyaki a hannun ƴan bindiga

Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da, alburusai huɗu na bindigar AK-47, babura guda uku, adduna guda biyu da wuƙaƙe masu kaifi guda biyu.

Kara karanta wannan

Rashin imani: Yadda 'yan bindiga suka kashe dan majalisa bayan karbar N100m

"Nasarorin da muka samu a cikin wannan wata sun nuna ƙoƙarin da muke yi wajen samar da tsaro a jihar Katsina."
"Ina jinjinawa jami’anmu bisa jajircewarsu wajen gudanar da aikinsu."
"Ina kuma miƙa godiya ta musamman ga Sufeto-Janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun, gwamnatin jiihar Katsina, da kuma manema labarai bisa ingantaccen rahoton da suke bayarwa."

- DSP Abubakar Sadiq-Aliyu

Nasarar abin a yaba ce

Wani mazaunin Kankara mai suna Idris Hussain ya shaidawa Legit Hausa cewa nasarar da ƴan sandan suka samu abin a yaba ne.

"Sun yi ƙoƙari gaskiya kuma abin a yaba ne nasarar da suka samu. Mu da muke zaune a inda ake samun matsalar mun san irin halin da mutane suke shiga."
"Muna yi musu fatan Allah ya ci gaba da ba su nasara a kan miyagu."

- Idris Hussain

Ƴan bindiga sun sace ƴan mata a Neja

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴa bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja da ke yankin Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'adda a jihar Zamfara

Ƴan bindigan a yayin harin da suka kai a ƙauyen Pandogari, sun hallaka wani jami'in tsaro na ƴan banga bayan sun harbe shi.

Miyagun ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da wasu ƴan mata guda shida waɗanda ke da ƙananan shekaru zuwa cikin daji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng