'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Daren Juma'a, Mutanen Gari Sun Masu Tara Tara, An Rasa Rai
- Ƴan ta'addan Lakurawa sun kai farmaki garin Gulma da ke ƙaramar hukumar Argungu a jihar Kebbi, sun kashe mutum
- Rahotanni sun nuna cewa ƴan ta'addan sun yi takansu yayin da suka ga mutanen gari sun haɗu, sun fito da niyyar kare kansu
- Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, ta tura dakaru domin kare dukiyoyi da rayukan mazauna garin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - An shiga fargaba a karamar hukumar Argungu ta jihar Kebbi bayan wani hari da ‘yan ta’adda suka kai a garin Gulma a daren Juma'a.
Ƴan ta'addan waɗanda ake kyautata zaton mayakan Lakurawa ne sun afkawa mutanen garin Gulma ne da misalin karfe 11:00 na dare a ranar Alhamis.

Asali: Original
A cewar shugaban ƙaramar hukumar Argungu, Aliyu Sani Gulma, mutum daya ya rasa ransa, yayin da wasu shida suka jikkata a harin, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutanen gari sun yi ƙoƙarin kare kansu
Ya ce miyagun ƴan ta'addan sun shiga garin a daidai lokacin da galibin mutane sun shiga gida sun kwanta barci kafin wayewar garin Juma'a.
"‘Yan ta’addan sun shigo garin yayin da mutanen ke barci. Sun kashe mutum daya sannan suka harbi wasu shida, yanzu haka an kwantar da su a Asibitin Tarayya da ke Birnin Kebbi,”
- in ji shi.
Ya kara da cewa ‘yan ta’addan sun ji tsoro, sun tsere zuwa daji da mutanen gari suƙa cire tsoro sannan suka taru suka tunkari maharan gadan-gadan.
"Mun sanar da hukumomin tsaro game da harin, kuma dakarun soji sun isa garin domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma," in ji ciyaman.
Yadda ‘yan sanda suka ɗauki mataki
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ‘yan sandan Kebbi, CSP Nafi’u Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Ya ce rundunar ta tura jami’an ‘yan sanda na musamman zuwa yankin domin tabbatar da tsaron mutane.
Sanata Aliero ya ce an fatattaki Lakurawa
Wannan harin ya zo ne bayan tsohon gwamnan Kebbi kuma Sanatan Kebbi ta Tsakiya, Adamu Aliero, ya bayyana cewa sojoji sun fatattaki kungiyar Lakurawa zuwa Jamhuriyar Nijar.
A cewarsa, hakan ya biyo bayan matakan ministan tsaro, Abubakar Badaru, da babban hafsan tsaro da sauran masu ruwa da tsaki suka ɗauka na murƙushe su.
Sanata Aliero ya yi gargadi cewa idan ba a dauki matakin gaggawa ba, yankin Arewa maso Yamma na iya fuskantar irin barnar da ta auku a Arewa maso Gabas.
"Yankin Arewa maso Yamma yana da yawan jama’a, filayen noma da kuma albarkatun ruwa. Saboda haka, dole ne a tabbatar da tsaron yankin kafin al’amura su tabarbare," in ji shi.
Sai dai bayan wannan harin na daren Juma'a, jami'an tsaro sun kai ɗauki garin Gulma kuma ana sa ran matakan da suka ɗauka zai kare aukuwar wani hari a gaba.
Sojoji sun murƙushe ƴan bindiga 20
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar hallaka ƴan bindiga sama da 20 a jihohin Kebbi da Sakkwato.
Sojojin sun samu wannan nasara ne yayin ɗa suka kai samame maɓoyar ƴan ta'addan, sun kuma ƙona sansanoninsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng