Matsin Lamba daga Sojoji Ya Tilastawa Turji da Amininsa Tserewa, An Fadi Halin da Suke ciki

Matsin Lamba daga Sojoji Ya Tilastawa Turji da Amininsa Tserewa, An Fadi Halin da Suke ciki

  • Sojoji sun kai farmaki kan ‘yan bindiga a dazukan jihar Zamfara inda suka ragargaza sansaninsu da ke bayan gari
  • Hare-haren sojojin ƙasa da na sama sun taimaka wajen dakile ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Yammacin kasar
  • An kashe hatsabiban yan bindiga kamar Kachalla Na Faranshi tare da mabiyansa a Zurmi, kuma an lalata sansanin Sani Black
  • Sojoji sun ci gaba da kai farmakin “Operation Show No Mercy,” suna ruguza sansanonin ‘yan bindiga, sun sa miyagu sun tsere

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Gusau, Zamfara - A cikin dazukan Jihar Zamfara, ana ci gaba da kai gagarumin farmaki don ragargaza sansanonin ‘yan bindiga da suka addabi yankin.

Tun daga ranar 2 ga Fabrairu, jami’an tsaro da goyon bayan hare-haren sama sun kai farmaki kan maboyar ‘yan ta’adda a Zurmi/Shinkafi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki masallaci, sun sace limami da masallata

Nasarorin da sojoji ke samu a dazukan Zamfara
Bello Turji da sauran yan bindiga sun tsere daga yankunan da suka boye. Hoto: Legit.
Asali: Original

An fatattaki Bello Turji daga sansanoninsa

Rahotan Zagazola Makama ya ce cikin nasarorin da aka samu shi ne kashe Kachalla Na Faranshi da mabiyansa yayin wani farmaki a cikin dazukan Karamar Hukumar Zurmi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata nasarar ita ce lalata sansanin Sani Black da ke Tunga Fulani Hills, sojoji tare da jiragen yakin sama suka lalata sansanin kuma suka kona gidansa.

A wata gagarumar nasara, jami’an tsaro sun sake kai farmaki sansanin Bello Turji, suka lalata sauran yankunansa, lamarin da ya tilasta masa tserewa.

Wani babban jami’in leken asiri ya ce manufar su ita ce kawar da ‘yan bindiga gaba daya.

"Ba za mu dakata ba har sai an gama da su."

- Cewar majiyar

Nasarorin da sojoji ke samu kan yan ta'adda

Ana ci gaba da kai farmakin “Operation Show No Mercy,” wanda ke nuna sabon salon yaki da ‘yan bindiga a Zamfara da yankin Arewa maso Yamma gaba daya.

Kara karanta wannan

'Diyar Ganduje ta samu babban mukamin gwamnati, majalisa ta aika sunaye ga Tinubu

Shekaru da dama, ‘yan bindiga sun fake a cikin dazukan Zamfara, suna amfani da su wajen kai hare-hare kan al’ummomi da kwasar ganima.

Sai dai da yadda wannan farmaki ke kara karfi, alama tana nuna cewar lokaci ya kure wa ‘yan bindigar da suka addabi jama’a tsawon shekaru.

Yayin da farmakin ke ci gaba, idanu sun koma kan dazukan Zamfara, ‘yan bindiga na cikin firgici, kuma zaman su ya kusa karewa.

Hafsan sojoji ya magantu kan ta'addanci a Arewa

Kun ji cewa Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana damuwa kan tabarbarewar tsaro, musamman yadda ake samun yan ta’adda da kudaden kasashen ketare

Janar Musa ya ce akwai wasu da ke daukar nauyin ta'addanci, ciki har da kudaden da ake samu ta garkuwa, fashi, da haramtattun hanyoyi.

Hafsan tsaron ya yi kira da a hada kai domin kawo karshen matsalolin tsaro, yana mai jaddada cewa Najeriya ta yi nasara kan ta'addanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.