Bayan Barau Ya Raba Tallafi, Abba Kabir Ya Mika Miliyoyi ga Matasan Kano

Bayan Barau Ya Raba Tallafi, Abba Kabir Ya Mika Miliyoyi ga Matasan Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya raba N400m ga kungiyoyin matasa 10 don inganta harkokin noma da samar da abinci
  • Kowace ƙungiya daga cikin 10 ta karɓi N40m, inda kowane mutum zai sami akalla N1m a matsayin jarin shiga gona
  • An gudanar da rabon kuɗin ne ƙarƙashin shirin ACReSAL da haɗin gwiwar Babban Bankin Duniya a jihar Kano

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta raba tallafin kuɗi na Naira miliyan 400 ga kungiyoyin matasa domin su rungumi harkokin noma.

Wannan tallafi wani ɓangare ne na shirin bunkasa noma karkashin ACReSAL tare da haɗin gwiwar Babban Bankin Duniya.

Abba Kabir
Abba Kabir ya raba tallafin noma ga matasan Kano. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Sanarwar hakan ta fito ne daga kakakin gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, a wata takarda da ya fitar ranar Alhamis a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi gari gari, sun kashe bayin Allah tare da sace mutane sama da 100

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba ya raba tallafi ga matasan Kano

An gudanar da bikin rabon tallafi a dakin taron Coronation da ke gidan gwamnatin Kano, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana dalilan bayar da kuɗi ga matasan Kano.

Gwamnan ya ce kowace ƙungiya daga cikin kungiyoyin matasa 10 da aka zaɓa za ta sami N40m, kuma kowane mutum zai karɓi aƙalla N1m don fara sana'ar noma.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce shirin ya ƙunshi ƙungiyoyin matasa da ƙungiyoyin manoma waɗanda aka zaɓa daga kananan hukumomi huɗu a Kano.

Ya ƙara da cewa an samar da shirin ne domin rage rashin aikin yi tare da samar da wadatar abinci a Kano da Najeriya gaba ɗaya.

Amfanin shirin ACReSAL a Kano

Gwamnan ya bayyana cewa shirin ACReSAL ya taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalolin muhalli a jihar Kano.

Ya buƙaci matasan da suka amfana da tallafin da su yi amfani da shi yadda ya dace, domin su zama masu dogaro da kai.

Kara karanta wannan

Jami'an gwamnatin El Rufa'i sun goyi bayansa, an zargi Uba Sani da bita da kullin siyasa

Haka zalika, ya umarci kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar Kano, Dr Dahir Muhammad Hashim, da ya ƙirƙiri sababbin shirye-shirye domin kare muhalli.

Abba Kabir ya ce jihar Kano za ta ci gaba da aiki tare da ƙungiyoyin duniya domin tabbatar da ci gaban noma da kare muhalli.

Kalaman masu ruwa da tsaki

A jawabin sa, kwamishinan muhalli, Dr Dahir Hashim, ya yi kira ga matasan da suka karɓi tallafin da su yi amfani da shi ta hanyar da ta dace.

Ya bayyana cewa akwai ƙungiyoyin bada tallafi na duniya da ke shirye su haɗa kai da jihar Kano idan aka sami nasara a wannan shiri.

Shi kuwa shugaban shirin ACReSAL na ƙasa, Alhaji Abdulhamid Umar, ya jinjinawa gwamnatin Kano bisa yadda take ƙoƙarin rage rashin aikin yi a tsakanin matasa.

Gwamnatin Kano ta kaddamar da shirin ne kwana daya bayan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya fitar da shirin tallafin noma ga matasan Arewa ta Yamma.

Kara karanta wannan

Masu koyo da haddar Kur'ani Mai Girma za su samu gata, Gwamnatin Kano ta faɗi shirinta

Rusau: Abba ya ziyarci Rimin Zakara

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kano ya ziyarci Rimin Zakara da jami'ar Bayero ta yi rushen-rushen da ya jawo mutuwar mutane.

A lokacin ziyarar, Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin gudanar da ayyukan raya kasa a Rimin Zakara da daukar nauyin wadanda aka kashe musu iyalai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng