Ana Tsaka da Neman Bello Turji, Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Dan Bindiga a Zamfara

Ana Tsaka da Neman Bello Turji, Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Dan Bindiga a Zamfara

  • Dakarun Fansan Yamma sun kashe hatsabibin dan bindiga, Kachalla Na Faranshi tare da mabiyansa a dajin Zurmi da ke Zamfara
  • Na Faranshi ya kware wajen shigo da makamai daga Mali da Nijar, sannan yana tallafa wa 'yan ta'adda a Arewa maso Yamma
  • Sojoji sun yi nasarar dakile hare-haren Na Faranshi, wanda dabarsa ta yi fice wajen garkuwa da mutane da safarar makamai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Dakarun Operation Fansan Yamma sun kashe fitaccen dan bindiga, Kachalla Na Faranshi, a harin da suka kai cikin dazukan Zurmi da ke jihar Zamfara.

An ce Kachalla Na Faranshi da wasu mabiyansa sun mutu yayin wani farmaki mai tsanani da sojoji suka kai dazukan yankin Zurmi.

Majiya ta yi magana da sojoji suka kashe hatsabibin dan ta'adda, Kachalla Na Faranshi.
Kachalla Na Farashi da mabiyansa sun gamu da ajalinsu a wani farmakin sojoji a Zamfara. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojoji sun kashe Na Faranshi da mabiyansa

Wata majiya ta tabbatar wa mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama cewa dakarun sun kashe 'yan ta'addan bayan musayar wuta.

Kara karanta wannan

2027: Kashim Shettima ya fadi yadda ya ke mu'amalantar Atiku a bayan fage

Majiyar ta nuna cewa Na Faranshi, wanda babban dan bindiga ne da ke da tawagarsa ya fito daga kauyen Shirgi da ke Maradi, Jamhuriyar Nijar.

Na Faranshi: Dan kasuwar da ya koma ta'addanci

Kafin ya shiga ta'addanci, Na Faranshi da mahaifinsa suna kasuwancin shanu, daga baya ya tsunduma cikin fasa kwauri da ta'addanci.

Tungarsa ta kasance cikin dajin Dutsen Kura, Kudu maso Yamma da Mashema a yankin Zurmi, kamar yadda rahoto ya nuna.

Na Faranshi ya shahara wajen shigo da makamai daga Mali da Nijar, yana raba su ga kungiyoyin ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma.

Ya taba hada kai da 'yan ta'adda a kasar Mali kuma ya yi aiki tare da dan bindigar nan, Bello Turji kafin ya kafa tasa kungiyar 'yan ta'addan.

Na Faranshi ya yi barazanar farmakar Zurmi

A ranar 23 ga Maris, 2024, Na Faranshi ya fitar da bidiyo yana barazanar kai hari a Zurmi tare da mabiyansa dauke da makamai masu hadari.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun fadi sunayen 'yan siyasa 3 da ke shirin ruguza gwamnatin Tinubu

Kungiyarsa ta yi fice wajen kai hare-hare, garkuwa da mutane da kuma safarar makamai a yankin.

A harin baya-bayan nan a dajin Zurmi, jami'an tsaro sun yi musayar wuta da su, inda suka kashe Na Faranshi da wasu daga cikin mabiyansa.

Sojoji sun taso Turji a gaba, ya tsere

A wani labarin, mun ruwaito cewa hatsabibin dan ta'adda, Bello Turji na ci gaba da yin wasar 'yar buya da sojojin Najeriya yayin da suka taso shi a gaba.

Rundunar sojojin ta ce yanzu Bello Turji ya rikice kuma yana ta neman wurin buya daga hare-harensu inda har ya gudu ya bar dansa aka kashe shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com