An Yi Babban Rashi: Jarumin Ɗan Sanda da Ya Addabi Boko Haram, ACP Dauda Ya Rasu
- Shahararren jarumin dan sandan Najeriya, ACP Dauda Buba Fika ya rasu a asibitin kasa na Abuja bayan doguwar rashin lafiya
- A matsayin kwamandan wani rukunin Mopol, ACP Dauda ya jagoranci hare-haren da dama inda ya kwato garuruwa daga ‘yan ta’adda
- Jarumi, ACP Fika ya samu raunuka a 2017 yayin fafatawa da ‘yan ta’adda, wanda ta kai shi kwanciya a asibiti har zuwa rasuwarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rahoto ya nuna cewa mataimakin kwamishinan ‘yan sanda (ACP) Dauda Buba Fika, da ya addabi Boko Haram a Arewa maso Gabas ya rasu.
An tabbatar da cewa, jajirtaccen jami'in dan sandan ya rasu ne a asibitin kasa na Abuja, da misalin karfe 3:30 na rana, a ranar Talata, 4 ga Fabrairu.

Asali: Twitter
Jarumin dan sanda, ACP Dauda ya rasu

Kara karanta wannan
'Ba su kai 900 ba': Kaduna Electric ya fadi adadin ma'aikatan da ya kora daga aiki
Babban mai sharhi kan lamuran tsaro a Arewa maso Gabas da Tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya sanar da rasuwar ACP Dauda hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zagazola Makama ya ce ACP Dauda ya shahara da jarumtarsa da jagoranci wajen kwato garuruwa da dama a Yobe da Borno daga hannun Boko Haram.
A matsayin kwamandan Mopol rukuni na 41, ya jagoranci hadin gwiwar jami’an tsaro wajen fatattakar ‘yan ta’adda tare da kwato garinsa, Fika.
Mutane sun yi alhinin rasuwar ACP Dauda
A shekarar 2017, ACP Dauda ya samu raunuka sakamakon harbin bindiga a lokacin wata arangama a Yobe, lamarin da ya kwantar da shi.
Jami’an tsaro, abokan aiki, da al’umma sun nuna alhinin rasuwarsa, yayin da suka bayyana shi a matsayin jarumin da ya sadaukar da rayuwarsa don kawo zaman lafiya.
Mutuwarsa ta bar babban gibi a fannin tsaron Najeriya, musamman a yaki da 'yan ta'adda a shiyyar Arewa maso Gabas.
Tarihi zai tuna shi a matsayin gwarzo, wanda ya taka rawar gani wajen tsare lafiyar al’umma da tabbatar da zaman lafiya a Arewacin Najeriya.
"An wulakanta ACP Dauda" - Datti Assalafiy
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani mai sharhi kan lamuran tsaro, da ake kyautata zaton dan sanda ne, Datti Assalafiy ya yi magana kan rashin lafiyar ACP Dauda Fika.
A Yulin 2019, Datti Assalafiy ya yi ikirarin cewa sojoji ne suka rabi ACP Dauda, sannan dan sandan ya sayar da gidansa domin nemawa kansa magani.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng