Yadda Boko Haram suka mamaye sabbin garuruwa a jihar Borno

Yadda Boko Haram suka mamaye sabbin garuruwa a jihar Borno

- Mutane da yawa sun rasa rayukan su sakamakon harin Boko Haram

- Yan ta'addan su sake kwace garin Gudunbari

- Anyi musayar wuri tsakanin yan ta'addan da sojoji

Yadda Boko Haram suka mamaye sabbin garuruwa a jihar Borno
Yadda Boko Haram suka mamaye sabbin garuruwa a jihar Borno
Asali: Facebook

Mutane da yawa sun rasa rayukansu a harin yan Boko Haram da suka kai garin Gudunbari na karamar hukumar Gualala a safiyar asabar.

Yan ta'addan su sake kwace garin bayan musayar wuta da sukayi da sojojin Najeriya.

Majiyar mu tace misalin karfe 5:00 na safe ne Yan ta'addan suka kwace garin.

A yanzu haka yan ta'addan suna yawon su a Gudunbari dake Guzamala domin sun kwace garin. Sun kona gidaje kuma sun kashe mutane. Mutane daruruwa suna garin Gubio, wasu kuma suna boye a dazuzzuka.

DUBA WANNAN: Kwankwaso ya kore ni daga PDP

A haka, Sanata Muhammad Ali Ndume ya nuna damuwar shi akan harin.

A zantawar da yayi da manema labarai, yace yana tsoron dawowar ta'addanci ga sojojin da kuma mutanen yankin.

"A tunani na, yafi kamata su maida hankali a Sambisa, Mandara da Dikwa /Gamboru inda ta'addancin yafi yawa" inji Ndume.

Ya zuwa yanzu dai sojoji sun ce sun kwato garuruwan daga hannun Boko Haram kuma sun fatattake su.

Shekaru kusan goma kenan da aka fara yakar Boko Haram, kuma babu alamar gamawa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel