Ajandar Boko Haram: Ashe wai suna so su kwaci Damasak, Monguno da Abadam cikin makonnin nan ne

Ajandar Boko Haram: Ashe wai suna so su kwaci Damasak, Monguno da Abadam cikin makonnin nan ne

- Yan ta'addan Boko Haram na shirin kai hari

- Garuruwa uku suke shirin kwacewa; Abadam, Damasak da Monguno

- A cikin kwanaki 20 masu zuwa suke shirin kai harin

Ajandar Boko Haram: Ashe wai suna so su kwaci Damasak, Monguno da Abadam cikin makonnin nan ne
Ajandar Boko Haram: Ashe wai suna so su kwaci Damasak, Monguno da Abadam cikin makonnin nan ne
Asali: Twitter

'Yan ta'addan Boko Haram na niyyar kwace garuruwa uku a jihar Borno nan da kwanaki 20 masu zuwa, kamar yanda majiyar mu taji.

Garuruwan sune Damasak, Abadam da Monguno.

Kamar yanda majiyar mu ta fannin tsaro ya sanar damu, yan ta'addan sun yanke hukuncin ne a taron da sukayi a Baga a ranar alhamis bayan da suka kwace garin. Inda sama da sojoji 700 suka bace kuma sama da 2,000 suka ritsa.

"Zasu kai harin ne a cikin kwanaki 20 masu zuwa. Kamar yadda suka fada a taron da suka yi a Baga a ranar alhamis," inji majiyar.

"Inda suke tunanin zai basu wahala ma Monguno ne. Suna jin Damasak da Abadam ba zasu sha wata wahalar kai harin ba. Zasu sha wahalar kai harin Monguno ne don akwai sojojin a nan."

An samu tabbacin wannan ikirarin daga wani mai aikin taimakon mutane, wanda yace tsoron harin ne yasa suke tunanin barin garuruwan uku a yanzu.

Abadam karamar hukuma ce a yammacin kogin Chadi. Babban birnin shi kuwa ne Malumfatori. Yan ta'addan sun taba kwace garin a watan Octoba 2014 amma sojoji sun kwato shi watan fabrairu na 2015.

DUBA WANNAN: Allah ma ba zai bari a kwace mulki daga hannun APC a 2019 ba - inji wani babban Sarki

Damasak shine babban birnin karamar hukumar Mobbar. Yana nan a mahadar kogin Yobe da Komadugu Gana, had da iyakar kasar Nijar.

Monguno ma karamar hukuma ce a Borno, babban birnin ta ne Monguno, garin su NSA Babagana Monguno. Kamar dai Abadam, yan ta'addan sun taba kwace garin a watan janairu 2015 amma sojoji sun kwato shi bayan wata daya.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel