Wani abu sai Najeriya: Jarumin dan sandan da ya yaki Boko Haram da ransa ya zama abin wulakantawa a kasar nan - Datti Assalafiy

Wani abu sai Najeriya: Jarumin dan sandan da ya yaki Boko Haram da ransa ya zama abin wulakantawa a kasar nan - Datti Assalafiy

Mutumin da kuke gani a kasa sunansa CSP Dauda Buba Fika, shine Kwamandan rundunar ta 41 ta 'yan sanda masu kwantar da tarzoma, wanda sansaninsu yake a garin Damaturu babban birnin jihar Yobe

CSP Fika dan sanda ne da ya bayar da rayuwarsa domin ya yaki 'yan kungiyar Boko Haram, saboda tsabar kishin yankinsa ne yasa ya nemi ayi masa canjin wajen aiki ya koma jiharsa, domin ganin ya kawo karshen 'yan ta'addar Boko Haram.

A shekarar 2016 lokacin da 'yan Boko Haram suka kwace wasu garuruwa a jihohin Yobe da Borno, shine ya jagoranci wata runduna ta musamman suka kwato garinsa Fika daga hannun 'yan ta'addar.

Ya kuma jagoranci wata rundunar 'yan sanda inda suka je suka kubutar da 'yan sanda 18 da 'yan Boko Haram suka yi garkuwa dasu.

"Yan Boko Haram sun kai masa harin kwanton bauna har sau hudu amma ya tsallake cikin ikon Allah.

A duk tarihin 'yan sandan da suka yi yaki da Boko Haram babu wanda ya nuna irin jarumtar shi.

Sai dai kuma karshen jarumtarsa ya zo ne bayan wasu gurbatattun sojojin Najeriya da suke aiki a jihar Yobe sun harbe shi ranar 13 ga watan Afrilun shekarar 2017, amma cikin ikon Allah bai mutu ba.

Kamar yaddaa jaridar Premium Times ta ruwaito, CSP Fika yayi magana da wakilinta a lokacin da yake kwance a gadon asibiti a birnin London, ya bayyana cewa akwai wata rana da yana tafiya da rundunar shi, sai wasu daga cikin yaranshi suka samu sabani da sojoji a cikin garin Damaturu.

KU KARANTA: To fah: Hadimin Ganduje na jam'iyyar APC ya yiwa masoyiyar Abba Gida-Gida wani muhimmin alkawari

Da isar sa gida, sai yaga sojojin sun shigo har gida sun ci zarafinsa kuma suka dauke shi suka wuce dashi sansaninsu da niyyar harbeshi, sai shugabansu ya hana su.

Sanadiyyar wannan matsala da suka samu ne yasa sojojin suka sake yi masa kwanton bauna lokacin yana tafiya da yaransa guda biyu suka bude musu wuta, a take suka kashe yaran san guda biyu, shi kuma suka harbeshi sau biyu a cinya.

Cikin ikon Allah sai wani babban soja yaje wurin shine yasa aka kai shi asibiti, sannan kuma babu jimawa kwamishinan 'yan sandan jihar yaji labari, yaje har asibitin, ya kuma umarci a kai shi asibitin Abuja domin bashi kulawa da ta kamata.

Yanzu haka dai wannan jami'in dan sanda yana kwance a asibiti a birnin Landan, ya kuma makance saboda wani aiki da aka yi masa a kwakwalwarsa.

Ya bayyana cewa yayi mamaki matuka da rundunar sojin kasar nan ta mance dashi, ya kuma kara da cewa ya san tabbas idan Buratai yaji labarin abinda ke faruwa dashi zai kawo masa dauki.

Yanzu haka dai ya sayar da gidansa da kadarorinsa domin nemawa kanshi lafiya.

Sannan yayi godiya ga hukumar 'yan sandan Najeriya da irin taimakon da take yi masa wajen biyan kudin jinyarsa a Landan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel