'Ku Nemi Gafara': Bashir Ahmad ga Masu Sukan Tikitin Musulmi da Musulmi, Ya Fadi Dalilansa
- Tsohon hadimin Muhammadu Buhari ya bukaci wadanda suka soki mulkin Muslim-Muslim na Bola Tinubu su nemi gafara
- Bashir Ahmad ya fadi haka ne bayan shugaban CAN na Arewa ya ce Kiristoci na jin dadin mulkin Tinubu a yanzu
- Yakubu Pam ya ce zaluncin da Kiristoci suka fuskanta a gwamnatocin baya ya ragu, yana yabawa Tinubu kan kokarinsa na hada kowa da kowa a mulki
- Ahmad ya ce ikirarin cewa tikitin Muslim-Muslim zai zalunci Kiristoci ko mayar da Najeriya tarin Musulunci karya ne, yana bukatar masu suka su janye kalamansu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon hadimin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci masu suka ga mulkin Muslim-Muslim na Bola Tinubu da su nemi gafara.
Bashir Ahmad ya bayyana hakan ne bayan Yakubu Pam, Shugaban Kungiyar Kiristocin Arewa (CAN), ya ce Kiristoci sun fi samun walwala a mulkin Tinubu.

Kara karanta wannan
Jerin ma'aikatun da wuraren da aka sanya wa sunan Bola Tinubu bayan hawansa mulki

Asali: Facebook
Kungiyar CAN ta yabawa mulkin Tinubu
Bashir Ahmad ya bayyana haka a cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba 29 ga watan Janairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan shugaban CAN a Arewa, Yakubu Pam ya ce zaluncin da Kiristoci suka sha a gwamnatocin baya ya ragu.
Pam ya jaddada goyon bayansa ga Tinubu, duk da cewa CAN ta nuna adawa da tikitin Muslim-Muslim yayin zaben 2023 bisa dalilin rarraba kasa.
A ranar Asabar, yayin da yake magana da ‘yan jarida, Shugaban CAN na Arewa ya yaba da yadda Tinubu ke tafiyar da mulkinsa cikin adalci.
Bashir Ahmad ya kalubalanci masu sukar Muslim/Muslim
Amma yayin da Pam ke yabawa Tinubu, Bashir Ahmad ya bukaci masu suka su janye kalamansu, yana cewa sun yada jita-jita maras tushe.
Da yake mayar da martani ga rahoton Vanguard, Ahmad ya ce ikirarin cewa mulkin Muslim-Muslim zai zalunci Kiristoci ko mayar da Najeriya kasar Musulunci karya ne.
“Wadanda suka zage mu saboda goyon bayan tikitin Tinubu/Shettima su fito su nemi gafara, domin duk zargin da aka yi cewa za a cutar da su ki mayar da Najeriya kan tsarin Musulunci karya ne.”
- Bashir Ahmad
An maka Bashir Ahmad a kotu
Kun ji cewa shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya kai karar Bashir Ahmad gaban kotu kan zargin bata masa suna ta hanyar kiransa 'dan ta'adda.
Bashir Ahmad ya wallafa maganganun a shafin sada zumunta yana cewa Nnamdi Kanu da masu goyon bayan sakinsa sun zama barazana ga kasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng