Muhimman Dalilai 3 da Suka Sa Aka Yi Ƙarin Farashin Man Fetur a Najeriya
Kimanin wata guda bayan samun saukin tsadar fetur a Najeriya, farashin kowace lita ya sake tashi a wurin lodin ƴan kasuwa.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Matatar hamshakin attajirin ɗan kauswar nan, Aliko Ɗangote ta sanar da ƙara farashin kowace lita a rumbuna, daga N899 zuwa N955 da N950 ga masu saye da yawa.

Source: UGC
A rahoton da Daily Trust ta wallafa ranar Juma'a, sabon farashi ya nuna an samu ƙarin kashi 6.17%, ko N55.5 a kan kowace lita, idan aka kwatanta da farashin baya watau N899.50.
Wannan ƙarin farashi na zuwa ne kimanin wata guda bayan rangwamen da ƴan Najeriya suka samu a lokacin da ake tunkarar bukukuwan kirismeti.
Yadda aka samu rangwame a karshen 2024
Idan za ku iya tunawa matatar Ɗangote ta sauke farashin fetur zuwa 899.50 a tsakiyar watan Disamba, 2024.
Kwanaki kalilan bayan haka kamfanin mai na ƙasa watau NNPCL ya bi sahun Ɗangote, shi ma ya rage farashin kowace lita zuwa ƙasa da N900.
Wannan rangwame da aka samu ya faranta ran ƴan Najeriya, inda suka fara fatan Allah ya sa hakan ya zama sanadiyyar da farashin zai ci gaba da karyewa a kasuwa.
Masana a ɓangaren harkokin mai a Najeriya sun yi hasashen cewa da yiwuwar fetur ya ci gaba da karyewa a kasuwa saboda gasar da ƴan kasuwa suka fara.
Sun yi wannan hasashe ne bayan matatar man Fatakwal ta dawo bakin aiki, ta shiga gogayya da matatun man ƴan kasuwa kamar ta Ɗangote.
Dalilan da suka sa fetur ya sake tashi
Duk bayan haka ne kwatsam matatar Ɗangote da kamfanin NNPCL suka fito suka sanar da ƴan Najeriya cewa an samu canji a kasuwa, don haka mai ya ƙara tsada.
A wannan babin, Legit Hausa ta tattaro maku abubuwan da suka jawo fetur ya ƙara tsada ƙasa da watanni biyu bayan an samu rangwame a Najeriya.
1. Tashin farashin ɗanyen mai a kasuwa
Babban dalilin da ya jawo tashin farashin man fetur a watan farko a shekarar 2025 shi ne yanayin kasuwar ɗanyen mai.
Kowace ganga ta ɗanyen mai da ake tacewa a fitar da man fetur ta ƙara tsada a kasuwar duniya a watan Janairun, 2025.
Matatar Dangote ta bayyana cewa ta yi karin farashin fetur ga 'yan kasuwa ne sakamakon tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
Rukunin kamfanonin Ɗangote watau Ɗangote Group ne ya wallafa dalilin da ya sa aka samu ƙarin a wata sanarwa da ya wallafa a shafin X.
A rahoton Reeuters, farashin kowace gangar ɗanyen mai na Brent wanda aka fi amfani da shi ya dawo $79 a ranar Laraba, 22 ga watan Janairu. 2025.
2. Karin kuɗin haraji a Najeriya
Tun kafin Ɗangote da NNPCL su sanar da ƙarin kwanan nan, dillalan man fetur sun yi hasashen cewa litar mai za ta ƙara tsada musamman a jihohin Arewa.
Kungiyar dillalai masu zaman kansu watau IPMAN ta hango cewa farashin fetur zai tashi zuwa sama da N1,000 saboda harajin da hukumar NMDPRA ta ƙaƙaba masu.
Shugaban IPMAN na shiyyar Arewa, Alhaji Salisu Ten Ten, ne ya bayyana hakan a wata hira da BBC Hausa.
Ya ce masu rumbunan mai sun kara farashi saboda karin haraji, wanda hakan ya tilastawa ƴan kasuwa duba yiwuwar yin ƙari a gidajen mai.
3. Faɗuwar darajar Naira a kasuwar canji
Darajar Naira a kasuwar hada-hadar kudi na ɗaya daga cikin abubuwan da ke taka rawa wajen tsadar man fetur.
Duk da gwamnatin tarayya ta fara cinikin ɗanyen mai da matatar Ɗangote a Naira, ana ganin har yanzun akwai kayan aikin da ke buƙatar canji kafin sayo su.
A watan Disamba lokacin da aka samu rangwame, Dala ta sauka zuwa kimanin N1,500 amma makonni bayan haka ta fara komawa gidan jiya.
A halin yanzu, farashin Dala a kasuwar bayan fage ya dawo N1,660/1$, yayin da aka yi cinikin kowace Dala kan N1,552.58 a kasuwar gwamnati, rahoton Business Post.
Gwamnati ta tsame hannunta a farashin fetur
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce a yanzu babu hannunta a duk wani abu da ya shafi ƙayyade farashin man fetur.
Ministan albarkatun man fetur, Heineken Lokpobiri ya bayyana yanayin kasuwa ne zai rika yanke nawa za a sayar da fetur ga ƴan Najeriya.
Asali: Legit.ng


