An Kashe Sojojin Najeriya 80 a Wani Artabu da Dakarun Biafra? Gaskiya Ta Bayyana

An Kashe Sojojin Najeriya 80 a Wani Artabu da Dakarun Biafra? Gaskiya Ta Bayyana

  • Wasu rahotanni da ke yawo sun nuna cewa cewa sojoji 80 na Najeriya sun mutu a sabon rikici da mayakan Biafra a jihar Abia
  • An rahoto cewa masu fafutukar kafa kasar Biafra na ci gaba da matsa lamba don ballewa daga Najeriya bisa zargin cin zarafi
  • Legit.ng Hausa ta duba idan akwai hujja game da wannan ikirari da ake yadawa na kisan sojojin Najeriya fada da IPOB

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abia - Rahotannin da ke yawo a watan Disambar 2024 sun nuna cewa an kashe sojojin Najeriya 80 a wani artabu da dakarun da ke fafutukar kafa kasar Biafra.

An ce 'wai' mayakan Biafra sun kashe sojojin ne a garin Ohafia na jihar Abia da ke a kudancin Najeriya a artabun da suka yi.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Sojoji sun kashe hatsabibin shugaban ƴan bindiga da yaransa a Katsina

Bincike ya gano cewa babu gaskiya a ikirarin cewa an kashe sojoji 80 a arangama da mayakan Biafra
Wasu rahotonni da aka yada a kafafen sada zumunta na cewa mayakan Biafra sun kashe sojojin Najeriya 80. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Matashiya kan kungiyar kafa Biafra

Biafra, wani yanki ne na Kudu maso Gabas da yunƙurin ballewarsa daga Najeriya a 1967 ya haifar da yaƙin basasa na tsawon wata 30 a cewar rahoton BBC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan yaƙin, an sake haɗa yankin da Najeriya, amma har yanzu ana cigaba da kiran kafa Biafra.

Gwamnatin tarayya ta ayyana kungiyar masu faftukar kafa Biafra (IPOB) a matsayin ƙungiyar ta'addanci kan ayyukan da take yi na tayar da zaune tsaye a yankin.

Ana zargin an kashe sojoji 80 a Abia

A wannan yanayin ne rahotanni suka bayyana a Facebook a Disambar 2024 inda suke cewa an kashe sojojin Najeriya 80 yayin arangama da mayakan Biafra a Ohafia, jihar Abia.

Wani Oku Biafra ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:

“Harbin bindiga a Ohafia: Mayakan Biafra da sojojin Najeriya sun yi arangama, sojojin Najeriya 80 sun mutu, yayin da Biafra suka rasa mayaka 3."

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta yi magana kan batun jefawa mutane bama bamai a Sakkwato

Saƙon ya haɗa da hotuna guda biyu: ɗaya na motar soja da aka lalata tare da wasu sojoji biyu, ɗaya kuma na tankar soja ce mai launin kakin soja.

Wasu kafafin sadarwa masu alaka da Biafra sun yada wannan rahoton a shafukansu daban daban.

Amma shin gaskiya ne an yi arangama tsakanin sojojin Najeriya da mayakan Biafra, kuma an kashe sojoji 80? Mun bincika.

An yi arangama tsakanin sojoji da IPOB?

Binciken da aka yi ta hanyar Google reverse image ya gano cewa sojojin Najeriya ne suka wallafa hoton farko a shafinsu na Facebook a 2019.

An gano cewa hoton na biyu ya fara fitowa ne a wata maƙala ta 2014 mai taken “Sojojin Najeriya da rikicin 'yan tada kayar baya,” wacce jaridar Vanguard ta wallafa.

Rahoton Africa Check ya nuna cwa wadannan hotunan ba su nuna wata arangama ta kwanan nan tsakanin sojojin Najeriya da mayakan Biafra ba.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Amnesty ta yi zargin ana son 'karasa' matashin da 'yan sanda suka jefawa gurneti

Babu gaskiya a rahoton kisan sojoji 80

Bincike a shafin yanar gizon sojojin Najeriya da kafafen sada zumunta ya nuna babu wata shaida game da ikirarin.

Haka nan, kafafen watsa labarai na gida suna bibiyar rikicin Biafra sosai, amma babu rahoto da ya tabbatar da harbin bindiga a Ohafia da aka kashe sojojin Najeriya 80.

Sojoji sun kashe mayakan IPOB/ESN

A wani labarin, mun ruwaito cewa dakarun sojin Najeriya sun ragargaji mayakan Biyafra da kuma 'yan haramtacciyar kungiyar tsaro ta Gabas (IPOB/ESN).

An ce sojojin Najeriya sun yiwa mayakan da ke fafutukar kafa kasar Biafra kifa daya kwala a musayar wutar da suka yi a Ejemekuru, karamar hukumar Oguta ta jihar Imo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.