'Sai Mun Tashi Tsaye': Sheikh Daurawa Ya Lissafa Alamomi 5 Na Lalacewar Matashi
- Sheikh Aminu Daurawa ya ce matashin da ba ya Sallah yana da babbar alamar lalacewa, musamman idan yana gudunta
- Rashin zuwa makaranta, ko dai ta boko ko ta addini, yana daga cikin manyan alamomin matashin da ke shirin lalacewa
- A cikin wani bidiyo Sheikh Daurawa ya lissafa alamomi biyar na lalacewar matashi ciki har da rashin sana'a da shaye-shaye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Fitaccen malamin addinin Musulunci na Arewa, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi magana kan tarbiya a tsakanin matasa.
Sheikh Aminu Daurawa ya shaida cewa alamomin lalacewar matashi guda biyar ne, inda kuma ya yi bayani dalla dalla a kan kowanne.
A wani bidiyon malamin da Mubarakh Sani ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheik Daurawa ya lissafa alamomin lalacewar matashin kamar haka:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Rashin yin Sallah
Sheikh Aminu Daurawa ya ce alamar farko ta lalacewar matashi ita ce rashin yin Sallaha, yana mai cewa:
"Duk matashin da za ka an kira Sallah biyar ba ya zuwa Sallah, ko ya ki yi, ko ya rika yin baya baya ko yana gudun Sallah, to ka samu babbsar alama ta cewa ya fara lalacewa."
2. Rashin zuwa makaranta
Malamin addinin ya ci gaba da cewa alama ta biyu ta gane lalacewar matashi ita ce rashin zuwa makaranta.
Sheikh Daurawa ya ce:
"Matashin da ba ya zuwa makaranta, ba boko ba mahammadiyya, to alama ce ta cewa an tafi."
3. Rashin sana'a ko aikin yi
Malam Aminu Daurawa ya ci gaba da cewa:
"Na uku idan ka ga ba shi da sana'a. Dole ya ci ya sha, ya rike waya babba, ya yi dinki, yana son ya yi budurwa ba shi da sana'a, to dole ya sace awakai, fankoki, fitilu, wayoyi na unguwa."
Malamin addinin ya nuna takaici yadda har makabartu yanzu matasa na shiga suna sace allunan kabari suna sayarwa saboda rashin sana'ar yi.
4. Shaye shayen miyagun kwayoyi
Alama ta hudu da malamin ya ambata ita ce shaye shayen kwayoyi, wacce ta zama ruwan dare a tsakanin matasan Najeriya.
Sheikh Daurawa ya yi nuni da cewa:
"To da matashi ya fara shaye shaye, magana ta tafi, ka ga ba ilimi, ba Sallah, ba sana'a ga shaye shaye sannan..."
5. Fada da iyaye
Malam Aminu Daurawa ya karkare lissafinsa a kan alama ta biyar, wadda ita ce rashin biyayya da kuma fada da iyaye da matasa ke yi.
Malamin ya ce ana samun matasan da kullum cikin fada suke da iyayensu, yana mai cewa:
"Kullum iyayen cikin kuka suke, ya dauko masu rigima, fitima da tashin hankali. Kullum ai sallama da uba da uwa, ya sace nata ya sace na uban, ya sace anguwa."
Sheikh Daurawa ya ba da labarin wata mata da ta yi baki, amma kafin bakin su tafi, yaranta sun sace takalmin daya daga cikin bakin.
Malamin ya ce ire iren wadannan matsaloli ne ke sa iyaye su rika yin kukan zuci har ma ta gai ga sun fara yiwa yaran nasu baki, suna la'antarsu da zaginsu.
Kalli bidiyon a kasa:
Abin da za a yiwa mahaifin da ya rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya lissafa wasu muhimman abubuwa 5 da ake so 'ya 'ya su yiwa mahaifinsu idan ya rasu.
A wani faifan bidiyo, Sheikh Daurawa ya ce an so 'ya 'ya su yawaita yiwa mahaifansu addu'a idan su rasu, su yi masu sadakatul jariya da ziyartar aminansu da sauransu.
Asali: Legit.ng