Jama'ar jihar Kano sun fara kokawa kan yawan satan allunan makabarta

Jama'ar jihar Kano sun fara kokawa kan yawan satan allunan makabarta

- Wasu mazauna a jihar Kano sun koka kan yadda sace-sace yayi yawa a makabartun jihar

- A wani yanki, mazauna da masugadin makabarta sun koka kan yadda ake sace allunan alama

- Sun bayyana zarginsu ga 'yan gwan-gwan dake tsince-tsincen karafa, su kuwa sun musa hakan

Masu kula da wata makabarta da ke Gwale a jihar Kano a arewacin Najeriya na ci gaba da kokawa kan irin yadda suka ce ana samun ƙaruwar sace allunan alamomi na kaburbura.

Masu kula da makabartar sun shaidawa BBC cewa tun kusan watanni uku baya ne suka lura ana yi wa shaida a kaburbura dauki dai-dai, yayin da wasu kuma allunnan suke ganinsu a lankwashe idan gari ya waye lamarin dake nuni da cewa an yi ƙoƙarin cirewa ne.

Wakilin jaridar a Kano Khalifa Shehu Dokaji wanda ya je makabartar kafa da kafa, ya ce ya ga kaburbura da dama da aka cire allunansu aka tafi da su, wasu kuma a allunan alamarsu lauye.

KU KARANTA: Baku isa ba: Shugaba Buhari ya gargadi 'yan bindigan da ke sace dalibai

Jama'ar jihar Kano sun fara kokawa kan yawan satan allunan makabarta
Jama'ar jihar Kano sun fara kokawa kan yawan satan allunan makabarta Hoto: BCC
Source: UGC

Danjuma Labaran na daga cikin masu hakar kabari a wannan makabarta ta Dandolo, ya kuma bayyana cewa tun da farko sun fara samun koke ne wajen jama'a dangane da batan allunan da suka sanya a kabuburan 'yan uwansu da aka binne a wannan makabarta.

''Muna zargin 'yan gwan-gwan ne ke zuwa su kwashe su, don sune suke yawo a nan wajen, sukan zo su wuce, kuma akwai gefen makabarta da suke irin waɗannan ayyukan'' in ji Malam Danjuma.

Sai dai wasu masu sana'ar ta tsince-tsincen kayan karafan wato gwan-gwan a wannan yankin, sun musanta wannan zargi da ake yi musu.

Jihar Kano dai na da tarin makabartu da dama da babu hasken wutar lantarki, abin da wasu ke ganin cewa kan taimaka wajen bada mafaka ga masu zuwa su aikata miyagun laifuka a cikinsu.

Jama'ar jihar Kano sun fara kokawa kan yawan satan allunan makabarta
Jama'ar jihar Kano sun fara kokawa kan yawan satan allunan makabarta Hoto: BCC
Source: UGC

A wasu lokuta a baya, an sha samun wadanda ke shiga makabartu a jihar da tsakar dare don tone gawarwaki, su ciri wasu sassan jikinsu da wata mummunar manufa.

Jihar Kano na da mai bawa gwamna shawara na musamman kan lamuran da suka shafi makabartu, amma duk da haka wasu 'yan jihar na kokawa kan yadda ake samun matsaloli irin wadannan

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Gobara ta yi kaca-kaca da wasu gidaje a jihar Borno

A wani labarin, Kwamitin da ke yaki da gurbatattun kwayoyi da abinci a Jihar Kano ya ce ya kwace tare da lalata kwayoyin magani na bogi da suka kai darajar naira biliyan shida a cikin shekara tara da suka gabata.

Shugaban kwamitin Gali Sule ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a hedikwatar kungiyar 'yan jarida ta Kano ranar Asabar, kamar yadda NAN ya ruwaito.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit

Online view pixel