Laifi 10 da matasan Najeriya suke da akan yadda rayuwar su zai zama nan gaba

Laifi 10 da matasan Najeriya suke da akan yadda rayuwar su zai zama nan gaba

- Na fara arkan laifi ne domin banda wadda zai biya mun kudin makarantan ja’mia

- Najeriya kadai ne aka gan matasa da basu da aiki kuma suna caca ido rufe

- Da ance su je makaranta domin rayuwar su ta gyaru, sais u koma aikin karuwanci domin su samu kudi

- A wasu jihar a Najeriya, matasa sun daoka cewar, idan sun fita a makaranta, za su fi samun kudi

Matasan Najeriya suke da laifi akan yadda rayuwar su zai zama nan gaba
Matasan Najeriya suke da laifi akan yadda rayuwar su zai zama nan gaba

Daya daga ciki abin da matasa Najeriya na so shi ne ya ba wasu laifi akan inkari da yake fiskanta a rayuwar shi. Kodayake, wasu na da laifi damuwar rayuwar su, ama bai kamata mutun ya juya fiska akan cewar, ya kamata matasan Najeriya su sake tunani.

Yadda yan cana suke fadi: “Wadda yaba wasu laifi akan rayuwar shi yana da dogon hanya a gaba. Wadda bai ba kowa laifi ba zai iso.”

Wannan Karin magana ya yi daidai da matasan Najeriya. Domin kulum sai da a ji wai: “Na fara arkan laifi ne domin banda wadda zai biya mun kudin makarantan ja’mia, ko “Babu tsammani cewar, matasan Najeriya za su yi nasara nan gaba,” da wau kalmomi da ba kai aka.

Tattalin arzikin na kowani kasa zai ma wasu amfani, wasu kuma ba za su ji dadin shi ba. Ama abin da ya fi muhiminci shi ne, mutum ya san yadda zai yi tunani mai zurfi domin cire kanshi a damuwar da yake kawowa kankanana ƙorafi.

Ga dalilin da ya sa wasu matasan Najeriya basu samu cingaba ba a rayuwar su da kuma mataki da yakamata su dauka da damuwar zai zama abin tarihi:

1. Rashin ra'ayi ko bidi'a akan arkan rayuwa

Akwai wani magana cewar, mutane za su rika samun abu nafito wa kamar da kowani lokaci da aka yi shi domin hanyar daya ake bi wajen yin abin. Rayuwar yanzu, ya kamat kowa ya nemi ilimin gizo gizo. Babu wani aiki da zaka yi da baya bukatan amfani da kwamfuta.

Acikin ƙarni (shekaru ɗari) nan, wasu matasa basu iya amfani da kwamfuta ba. Basu iya aiki akai ba. Domin aka, suna baya. Wayanan mutane za su cigaba da bada ƙorafi cewar, shugaban kasa Muhammadu Buhari bai yi komai ba tun da ya zo mulki. Suna wannan, sauran suna tunani yadda za su fita a talauci da kuma dena yin korafi.

2. yawan shan giya

KU KARANTA: Sojoji sun samu gagarumar nasara, sun cafke mutumin dake yi ma Boko Haram leƙen asiri

Nan gaba matasa Najeriya yana lilo. Kalakala giya ya karbi arkan rayuwar su. Wasu abubuwa na sha dinna suna zuwa da yawan giya aciki da zai iya bata musu anta. Matasa suna gani da sun sha wannan giya, duk damuwar su sun tafi. A gaskiya, baa aka bane. Wayanan giya sun a kara musu damuwa ne domin tunani yadda za su fita a talauci zai ragu.

3. Caca

A Najeriya kadai ne aka gan matasa da basu da aiki kuma suna caca ido rufe. Misali, matasa da yakamata ya nemi dan kudi na fara sana’a ba zai yi aka ba. Ya fi mishi ya nemi kudin da zazi yi caca da shi. Daga baya sai ya rasa kudin. Zai cigaba da roko iyaye shi su bashi kudin kashewa ko ma ya fi shekara 30.

4. Rayuwa na almubazzaranci

Wasu matasa suna rayuwa da ta fi samun da suke. Wasu sun gaji dukiya ne daga wurin uba ko uwa ama za su yi banza da su akan mata, wasu rayuwa da ba kyau. Wanna hali zai cigaba har duk kudin zai kare bas u yi abin kirki da su ba. Da sun rasa ko anini a adjuhun su, sai su juya suna ganin laifi yan uwa, wasu ma suce iska ne ke damunsu.

5. Zina

Abin bakin ciki shi ne yadda yan mata suna arkan karuwanci. Ana ce musu suna saida jiki. Da ance su je makaranta domin rayuwar su ta gyaru, sais u koma aikin karuwanci domin su samu kudi. Wasu su samu cuta kamar ciwon kan’jamo da wasu cututuka da ana samu ta aka.

6. Fada a lokacin siyasa

KU KARANTA: An fatattako wani Dan Najeriya daga Amurka

Najeriya ne ya ke da lamba matasa masu taimaka ma yan siyasa domin rikita da ya fi na ko wani kasa yawa. Ba sai mun kirkiro wani sheda ba domin kafa wannan magana. Wannan zahiri ne idan siyasa ya zo. Ko wani dan siyasa da yake da suna, na da nashi kungiyar yan rikita zabe.

Akwai kira kulum na gayawa matasa kar su bar a yi amfani da sub a wajen siyasa. Matasan Najeriya ba su ji domin dan kudin da masu siyasa ke mika musu. Yawanci matasa su mutu garin neman kujera ma dan siyasa da ya ci ya koshi, yaran shi na kasan Turai.

7. zaben banzayen mutane a matsayin wadda za su rika bi da kuma gyara rayuwan su da su

Maimako su gyara rayuwar su da mutanen kirki, sais u ta bin mawaki, masu wakan da zai raba mutane ya kuma jayyo kiyyaya. Su bi rayuwar masu satan kudin gwamnati. Kalillan matasa suke duba rayuwar mtane masu albarka da yakamata a bi.

8. Zaman rayuwar na rude kai da karya

Duk mutanen da sun zama a zo a gani yanzu, sun biya da gumi su ne. bataba gan wani baban mutum a tarihi da bai da abin fada, irin wahala da ya sha kafin ya samu. Idan b aka sha wuya ba, ba zaka moore ba. Matasa na yanzu, ba so so abin da zai basu wahala ba komin kankanta shi. Sun dauka komai zai zo musu cikin sannu a hankali. Babu hakuri a aure, aiki komai sun a da gaggawa.

9. Ba sua san zuwa makaranta

A wasu jihar a Najeriya, matasa sun daoka cewar, idan sun fita a makaranta, za su fi samun kudi, a nasu tunani, ya fi sauri. Idan ka yi magan, sais u yi misali da mai kudin duniya da Afirka; Bill Gates da Aliko Dangote cewar, basu gama makaranta ba kafin suka yi kudin su. Abin da basu gane bas hi ne, mutane biyu nan, sun a da ilimin akan abin da suka zaba su yi kafin suka zama abin da su zama yanzu.

10. Rashin kula da al’hada na gida

Matasa sun dibi al’hada da ba namu ba sun sa akai, su jawo wando su har kasa duwawu su ce ‘sagging’, ba al’hada mu ba ne. Muna koya abin da ba zai mana amfani ba daga kasar waje. Yadda ake magana da ba dadi da shirin su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng