Shaye-shaye tsakanin matasan arewacin Najeriya yana tsoratarwa – In ji Uwargidar gwamnan Bauchi
Uwargidar gwamnan jihar Bauchi ta ce karuwar yawan shaye-shaye a tsakanin matasan arewacin kasar yana tsoratarwa. Ta ce matan gwamnonin arewa a taron da suka gudanar a Kogi sun tattauna yadda za a magance matsalar baki daya.
Uwargidar gwamnan jihar Bauchi wanda ita ne kuma shugaban kungiyar matan gwamnonin yankin arewa, Hajiya Hadiza Muhammad Abdullahi Abubakar ta bayyana karuwar yawan shaye-shaye a tsakanin matasan arewacin kasar nan a matsayin abin tashin hankali.
Da take zantawa da manema labarai a lokoja, babban birnin jihar Kogi bayan kammala taron matan gwamnonin arewa wanda aka yi a jihar, Hajiya Hadiza ta bayyana cewa sun gudanar da taron ne dangane da yadda ake samu karuwar yawan shaye-shaye tsakanin matasa musamman matan arewacin kasar a sassan daban daban na yankin.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa, Uwargidar jihar Bauchi ta ci gaba da cewa wannan babban kalubale ne a yankin.
KU KARANTA: Zagi da aibanta shugabanni bashi zai sa abubuwa su canza ba - El-Rufai ga matasa
Hajiya Hadiza ta kuma bayyana cewa matan gwamnonin sun tattauna batutuwa da dama dangane da yadda za a magance matsalar baki daya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng