An Shiga Tashin Hankali a Kaduna yayin da Wata Mata Ta Kashe Ƴarta da Maganin Ɓera
- Mercy Michael ta gurfana a kotu kan zargin kashe 'yarta da maganin bera, lamarin da aka ce ya faru a ranar 10 ga Disamban 2024
- Hukumar NSCDC ce ta gurfanar da wanda ake zargi, inda ta bayyana cewa an fara kai rahoton lamarin cibiyar Salama a Kaduna
- Alkalin kotun bai saurari rokon wanda ake zargi ba, inda ya umarci mai gabatar da kara da ya tura karar ga daraktan shari’ar jihar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna: Wata kotun majistare a Kafanchan, jihar Kaduna, ta bayar da umarnin tsare wata mata mai suna Mercy Michael kan zargin kashe 'yarta da guba.
Hukumar NSCDC ce ta gurfanar da Michael kan zargin kisan kai, wanda ya saba da Sashe na 189 na dokar laifuffuka ta jihar Kaduna.
Yadda mata ta kashe 'yarta a Kaduna
Mai gabatar da kara, Marcus Audu, ya shaida wa kotu cewa an kai rahoton lamarin ne ofishinsu a ranar 11 ga Disamba inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Audu ya ce Mercy Michael ta bai wa diyarta 'yar watanni takwas gubar kashe beraye a ranar 10 ga Disamba.
Yarinyar ta mutu a washe garin ranar bayan kai ta asibitin Kafanchan, a wani yunkuri na ceton rayuwarta.
Kotu yi hukuncin kan hurumin karar
An fara kai rahoton lamarin ga cibiyar bin kadin cin zarafin dan Adam ta Salama da ke a Kafanchan, kafin a mika shi ga NSCDC don bincike.
Alkalin kotun, Samson Kwasu, bai saurari rokon wacce ake zargin ba, domin kotun ba ta da hurumin sauraron karar.
Samson Kwasu ya umarci mai gabatar da kara da ya tura takardar ga daraktan shari’a na jiha domin samun shawarar doka kafin 17 ga Disamba.
Uwargida ta kashe mijinta da maganin bera
A wani labarin, mun ruwaito cewa wata yarinya 'yar shekara 16 da aka ce uwargida ce ta halaka mijinta ta hanyar sanya mashi maganin bera a abinci.
Lamarin wanda aka ce ya faru a kauyen Shittar dake karamar hukumar Danbatta na jihar Kano ya haifar da ce-ce-ku-ce kan illar yiwa yara mata auren dole.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng