Soyayya ta koma kiyayya: Uwargida yar shekara 16 ta kashe Mijinta da maganin ɓera a jihar Kano
Auren dole ya haifar da wani mummunan lamari a tsakanin masoya a jihar Kano, inda a yanzu haka ake shari’ar wata Uwargida mai shekaru 16 ta hallaka mijinta dan shekara 35 ta hanyar dafa masa abinci da maganin bera, inji rahoton Daily Trust.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a kauyen Shittar dake karamar hukumar Danbatta na jihar Kano, amma ana shari’ar kisan mijin da matarsa ta yi a Kotun majistri na mai shari’a Alkali Fatima Adamu dake birnin Kano.
KU KARANTA: Ina gwanin wani ga nawa: Wani hamshakin Farfesan jami’ar ABU ya samar da maganin zazzabin cizon Sauro
Dansanda mai kara, Auwal Mijinyawa ya bayyana ma Kotu cewar wani Maigida mai suna Auwalu Isah ya gamu da ajalinsa a ranar 22 ga watan Afrilu bayan ya ci abincin da matarsa ta girka masa,sai dai sufeta Auwalu yace matar ta zuba maganin bera a cikin abincin.
“Bayan mijinta ya ci abincin, nan take ya fadi matacce sakamakon gubar da ta cakuda da abincin da ta girka masa.” Inji Dansanda mai shigar da kara Auwalu. Sai dai Uwargidar ta musanta zargin kashe mijinta da ake yi mata.
Bayan sauraron dukkanin bangarorin, Alkali Fatima ta aika da uwargidar zuwa gidan Kurkuku na kananan yara, sa’annan ta dage sauraron karar zuwa ranar 7 ga watan Yuni
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng