Amarya ta kashe 'yayan kishiyarta 3 da guba a jihar Yobe, an damke ta
- Ana zargin Matar aure da laifin sanya guba cikin abincin da yaran kishiyarta suka sha
- Jami'an yan sandan jihar sun damketa kuma an fara bincike
- Tuni an yi jana'izar yaran a jihar Yobe
Potiskum - Hukumar yan sanda a jihar Yobe ta damke wata matar aure yar shekaru 22, Khajida Yakubu, kan laifin kashe 'yayan kishiyarta uku da guba.
Wannan abu ya faru ne ranar Juma'a a unguwar Makara-Huta dake karamar hukumar Potiskuma a jihar, rahoton Leadership.
Yaran sun sha guban ne cikin Shayin da kishiyar mahaifiyarsu ta shirya musu.
A jawabin da kakakin yan sandan jihar Yobe,ASP Dungus Abdulkarim, ya saki, ya tabbatar da cewa an damketa.
A cewarsa, Matar da kanta ta garzaya da yaran asibiti bayan da suka sha Shayin misalin karfe 9 na safe amma uku sun rigamu gidan gaskiya, saura 1.
Dungus yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Tuni dai yan sanda sun kaddamar da bincike domin gano abinda ya faru domin hukuntata."
Yaran da aka kashe sune; Zainab Alhaji Haruna (7), Ahmed Alhaji Haruna (9), Umar Alhaji Haruna (12), da Maryam Alhaji Haruna (11).
Yobe: Jama'ar da jirgin NAF ya yi wa luguden wuta suna bukatar diyya
A bangare guda, Iyalan wadanda mummunan lamarin da ya faru a jihar Yobe da su sakamakon luguden wutan da jirgin NAF ya so yi kan 'yan ta'addan Boko Haram, sun bukaci gwamnatin tarayya da ta biya su diyya.
Sun alakanta bukatarsu da dalilin cewa, gwamnati a kowanne mataki a Najeriya ba ta cika biyan diyya ba ga jama'a da aka yi wa barna.
Daga ciki mutum takwas da suka rasu, tsoffafi uku da wata mata wadanda suka bar kananan yara. Akwai yara kanana hudu da suka rasa rayukansu da kuma wasu gidaje da suka kone.
Asali: Legit.ng