Duniya ina zaki da Mu: Wata Mata ta kashe ƴarta da haɗin bakin Saurayinta
- Saurin fushi ya sanya wata budurwa kashe 'yarta guda da ta haifa
- Kuma yanzu haka ido tuni ya rana fata bayanda da suka shiga komar 'yan sanda
Rundunar Ƴan sanda ta jihar Niger ta damke wata Mata mai suna Fatima Adamu da kuma tsohon saurayinta Usman Mohammed bisa zargin kashe ƴarta.
Lamarin dai ya faru ne a ƙauyen Egbati dake ƙaramar hukumar Agaie a jihar ta Niger.
An rawaito cewa tsohon Saurayinta ne ya tamaka mata wajen haɗa jiƙe-jiƙen da ta ɗurawa ƴarta ta mai shekaru 5 domin hallaka ta.
Bincike dai ya nuna cewa, Mahaifiyar yarinyar da Saurayin nata sun jefar da gawar yarinyar ne a daji ba tare da wasu sassa na jikinta.
KU KARANTA: Hanyoyi 4 da ake kawar da radadin cizon cinnaka cikin gaggawa
Waɗanda ake zargin dai sun shaidawa majiyarmu ajiya Talata cewa, sun shayar da yarinyar ne magani mai ɗauke da guba a cikinsa.
"Ina sane na kashe ta, don na tsane ta, duk sanda na ganta haushi nake ji sosai. Sai muka haɗa baki da Saurayi na Mohammed to bata guba." Fatima ta faɗa,
kana ta ƙara da cewa,"Kawai na farka ne wata safiya naji ina son kashe ta, ni ma ban san dalilin da yasa na kashe yarinya ƙarama ba, ba tare da aikata laifin komai ba. Ina roƙon Allah ya gafartamin don wannan babban zunubi ne."
Shima Saurayin nata da tuni ya shiga hannu, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
"Ni na harhaɗa maganin mai dauke da guba a ciki na bawa Fatima don ta kashe ta yarinyar. Amma nayi nadama." a cewar Mohammed.
Kakakin Ƴan sanda na jihar Muhammad Abubakar, ya bayyana cewa, waɗanda ake zargin sun amsa laifukan nasu yayin da ake tuhumarsu. Kuma da zarar an kammala bincike zasu miƙa su gaban kuliya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng