‘Abin da Oshiomhole Ya Fada Mani a Sirrance da Muka Hadu a Majalisa’ Inji Bello El Rufai
- Honarabul Bello El-Rufai ya hadu da Adams Oshiomhole wanda yake tsananin girmamawa kamar ubansa
- Kafin tsohon shugaban na APC ya zama Sanata, Hon. Bello El-Rufai ya yi aiki a matsayin babban hadimin
- Sanata Uba Sani wanda shi ne gwamnan Kaduna a yau, ya ka shi majalisa da ya lashe zabe a 2019
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - ‘Dan majalisar tarayya, Bello El-Rufai ya na cikin matasan ‘yan siyasar da tauraruwarsu ta ke haskawa a halin yanzu.
Honarabul Bello El-Rufai mai wakiltar Kaduna ta Arewa a majalisar wakilan tarayya ya shahara har a wasu mazabu da jihohi dabam.
Adams Oshiomhole ya hadu da Bello El-Rufai
A ranar Asabar, Bello El-Rufai ya yi amfani da shafin X, ya ba da labarin wata haduwa da ya yi da tsohon gwamna, Adams Oshiomhole.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malam Bello ya bayyana cewa Adams Oshiomhole yana cikin Sanatocin da ya fi kauna a majalisa kuma ya na yi masa kallon uba.
Oshiomhole ya yi tambaya game da El-Rufai
‘Dan majalisar wakilan ya ce Oshiomhole ya tambaye shi halin da mahaifinsu yake ciki, kuma ya yabawa irin kokarinsa a majalisa.
Da ya nemi jin halin da tsohon gwamnan na jihar Kaduna yake ciki, Bello ya fadawa Oshiomhole cewa yana nan lafiya kalau.
Bambancin Bello da Nasir El-Rufai
‘Dan majalisar na APC ya yi kokarin nunawa Kwamred Oshiomhole bambancin da ke tsakaninsa da mahaifinsu, amma bai yarda ba.
Shi tsohon shugaban na kungiyar kwadago a Najeriya watau NLC yana ganin marabar Bello da mahaifin nasu kawai shi ne tsawon jiki.
Maganar Bello El-Rufai a X
"Tare da daya daga cikin Sanatocin da na fi kauna kuma tamkar uba a wurinmu. Mai girma Sanata (Kwamred Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan Edo.
"Ya tambayi ya Mallam (Nasir El-Rufai) yake ciki, sai na fada yana nan lafiya kalau.
"Daga nan sai ya ce in cigaba da yin ayyukan kirki kuma ya ga wasu bidiyoyina. Na fadawa shugabanmu cewa na fi Malam saukin kai.
"Mai girma Sanata sai ya ce mani ‘sak shi ka ke,’ sai ya yi mani rada cewa, sai dai kurum ka fi shi tsawo.
- Bello El-Rufai
A karshe matashin ‘dan siyasar ya godewa Oshiomhole da wadannan kalaman kara karfin guiwa da shawarwarin da ya ba shi.
Gwamnatin Bola Tinubu da 'yan Arewa
Kun ji labari saboda kin jawo Malam Nasir El-Rufai da Rabiu Kwankwaso ake zargin Bola Tinubu da yakar manyan ‘yan siyasar Arewa.
Maida hedikwatar wasu ma’aikatu kamar FAAN da kuma bangarorin bankin CBN zuwa garin Legas bai yi wa mutanen Arewa dadin ji ba.
Asali: Legit.ng