Tinubu Ya Yi Rabon Mukamai, Ya Ba Malamin Musulunci Matsayi a Gwamnatin Tarayya
- Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin sabon shugaban hukumar NUC mai alhakin kula da jami’o’i a Najeriya
- Mista Bayo Onanuga ya fitar da sanarwa cewa Shugaban kasa ya ba Farfesa Salisu Shehu mukami a gwamnati
- Yazid Shehu Umar Danfulani zai jagoranci gidauniyar shugaban kasa domin aikin ma’adanai da hako gwal
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
FCT, Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya nada sababbin shugabannin wasu hukumomin gwamnatin tarayya.
A yammacin Juma’a ne labari ya tabbata cewa Bola Ahmed Tinubu ya nada shugabannin da za su rike NUC, NERDC da sauransu.
Onanuga: Bola Tinubu ya yi nadin mukamai
Bayo Onanuga a matsayinsa na Mai magana da yawun shugaban kasa ya fitar da sanarwar a shafinsa na X watau Twitter.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Bayo Onanuga ya ce Bola Tinubu ya amince da nadin sababbin shugabanni a NUC da kuma NERDC a ranar Juma’ar nan.
An kuma nada sabon shugaban da zai jagoranci shirin SMDF/PAGMI da NEPAD a Najeriya.
Bola Tinubu ya nada shugaban hukumar NUC
Bayo Onanuga ya ce an zabi Abdullahi Yusuf Ribadu ya zama sabon shugaban hukumar NUC mai kula da jami’o’in da ke Najeriya.
Kafin nada shi a wannan mukami, Farfesa Abdullahi Yusuf Ribadu ya taba zama shugaban jami’ar fasaha ta tarayya da ke Yola.
Farfesa ya kuma taba jagorantar jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa a Jigawa, shi ne ya canji Farfesa Abubakar A. Rasheed.
Tun da Farfesa Abubakar A. Rasheed ya yi murabus, sai yanzu NUC ta samu shugaba.
The Cable ta ce malamin musuluncin nan, Farfesa Salisu Shehu shi ne wanda aka nada a matsayin shugaban hukumar NERDC.
Yanzu haka Farfesan shi ne shugaban jami’ar Al-Istiqamah da ke Sumaila a jihar Kano.
Tinubu ya nada shugabannin SMDF/PAGMI da NEPAD
Rahoton Premium Times ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya nada Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri a matsayin shugaban NEPAD.
Shi kuma Yazid Shehu Umar Danfulani wanda ya yi karatu a Najeriya da jami’ar Hertfordshire shi ne shugaban shirin SMDF/PAGMI.
Bola Tinubu ya ba Daniel Bwala mukami
A watan jiya aka ji labari cewa Bola Tinubu ya ba Daniel Bwala mukami a gwamnatinsa bayan watanni da ya bar Atiku Abubakar.
Lokacin yakin zaben 2023, lauyan ya bar jam’iyyarsa ta APC da sunan an tsaida musulmi da musulmi takarar shugabancin kasa.
Asali: Legit.ng