Gwamnati Ta Haramta Bugawa da Sayar da Ruwan Leda? Jami'in Gwamnati Ya Yi Magana
- Gwamnatin Legas, ta hannun kwamishinan muhalli, Tokunbo Wahab, ta bayyana cewa ba ta da shirin haramta ruwan leda a jihar
- Tokunbo Wahab ya musanta cewa jami'an gwamnatin Legas ne aka gani a bidiyo suna kamen ruwan leda a kasuwannin jihar
- Salim Isah, manajan gidan ruwan Dantafiya Table Water da ke Hayin Rigasa, ya yi ikirarin cewa talaka ya dogara ne da ruwan leda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Ana ta yada jita jitar cewa gwamnatin Legas ta haramta bugawa da sayar da ruwan leda a lungu da sakunan jihar.
Wani bidiyo da yake yawo a soshiyal midiya ya nuna wasu 'jami'ai' suna kwace ruwan leda a kasuwanni, lamarin da ya jawo jita jitar.
Kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa na Legas, Tokunbo Wahab ya yi martani a shafinsa na X, inda ya ce jita-jitar ba ta kai balle gindi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legas ba ta haramta ruwan leda ba
Gwamnatin jihar Lagos, ta hannun Tokunbo Wahab, ta tabbatar da cewa ba ta da wani shiri na hana bugawa ko sayar da ruwan leda.
Wahab ya musanta zargin cewa jami'an da aka gani a bidiyon suna aiki ne daga gwamnatin jihar Lagos, yana mai cewa gwamnati ba ta aiki kowa ba.
Ya ci gaba da cewa, gwamnati tana aiki kan yadda za a magance sharar roba da matakan da suka dace, ba tare da shirin haramta ruwa na leda ba.
Su wanene a cikin bidiyon?
Kwamishinan ya bukaci al'umma da su yi watsi da duk wani rahoto ko jita-jita da ke nuna cewa gwamnati ta haramta ruwan leda a jihar Legas.
"Bayan gudanar da bincike, mun gano cewa jami'an da ake magana akai suna daga hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC).
Ayyukansu na daga cikin aikin hana amfani da ruwan leda da bai dace da ka'idojin NAFDAC ba, kuma wannan yana da mahimmanci wajen lafiyar jama'a."
- A cewar kwamishinan.
Kalli bidiyon da Timi of Lagos ya wallafa kan kwace ruwan leda a Legas:
"Da ruwan leda talaka ya dogara" - Dantafiya
Salim Isah, manajan gidan ruwan Dantafiya Table Water da ke Hayin Rigasa, ya shaidawa wakilinmu cewa talaka ya dogara ne da ruwan leda a yanzu.
Salim Dantafiya ya yi nuni da cewa gidaje da dama ba sa iya samun ruwan famfo, don haka dole su nemi ruwan leda wanda shi ne mafi tsafta a kan na rijiya.
A yayin da ya yi kira ga gwamnatocin jihohi su horar da matasa tare da basu jari kan sana'ar ruwan leda, ya koka kan tsadar kayayyakin yin kasuwancin a yanzu.
Sali ya ce:
"Shekarar da ta wuce muna sayen ledar jera ruwan a kan N4000, amma yanzu ta koma N13,000. Ledar ruwan kanta ta koma N3,700 duk 1kg sabanin N800.
"Sannan ka duba yadda fetur ya yi tsada, ga babu wutar lantarki. Abin lura a nan, gidajen ruwa na kokari sosai, tsadar kayan tana wajen shagunan da ke sayarwa daya daya."
Kungiya ta kara kudin ruwan leda
A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar masu buga ruwan leda (ATWAP) sun sanar da batun karin farashin ko wacce jaka, daga N150 zuwa N200.
Shugaban kungiyar na yankin Oye-Ekiti da Ikole-Ekiti, Tale Oguntoyinbo ya sanar da hakan ta wata takarda a Oye-Ekiti inda ya sanar da dalilan tashin farashin.
Asali: Legit.ng