Na gwammace sayar da ruwan leda dana dinga zina ana biyana - Cewar wata dalibar jami'a
- Paris Diamond daliba ce mai karantar fannin jarida a kwalejin ilimi na Alvan Ikoku da ke Owerri a jihar Imo
- Diamond na siyar da ruwa, shinkafa, tana yin kitso da sauran kananan kasuwancinta don ta tsira da mutuncinta wajen daukar nauyin karatunta
- Ta bayyana cewa, sau da yawa jama'a na ce mata wannan kasuwancin bai dace da ita ba, amma ta ce hakan ya fi mata karuwanci
Paris Diamond daliba ce mai karantar fannin jarida a kwalejin ilimi na Alvan Ikoku da ke Owerri a jihar Imo. Dalibar mai shekaru 19 a duniya na tallar ruwa, tana siyar da shinkafa a makaranta duk a cikin kananan kasuwancin da take yi don samun kudi, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.
A yayin da ta wallafa hotunanta a shafin Facebook dinta a ranar Lahadi, Diamond ta bayyana tana tallar ruwa kuma ta ce wannan sana'ar ta fi mata a kan karuwanci.
"Ina siyar da ruwa ne don in samu kudin siyan litattafai a makaranta kuma wasu lokutan na kan kashe matsalolin gaba na. Ina zuwa kasuwa a kowacce Juma'a da yamma, safiyar Asabar da kuma ranakun Lahadi bayan na dawo daga coci.
KU KARANTA: A karon farko 'yan fim din Hausa dana kudancin Najeriya za su fitar da wani shahararren fim da suka yi tare
"Ina jin dadin sana'ata don a nan nake samun kudin takardu. Wannan sana'ar ta fi min a kan karuwanci. Gaskiya ina gayu na amma kuma siyar da ruwa ai kasuwanci ne. Ina siyar da jaka bakwai zuwa takwas a kowacce rana." Diamond ta ce.
Ta kara da cewa, "wasu lokutan mutane na cewa kasuwancin bai dace da ni ba. Na kan yi dariya kawai. Ni daliba ce kuma marubuciya. Na wallafa litattafai biyu amma rashin kudi yasa na kasa wallafa su don siyarwa.
"Wasu lokutan idan na koma gida, ko karatun bana iya wa saboda gajiya. Ina siyar da ruwa, shinkafa, takalmi, ina yin kitso da wasu kananan kasuwancin da ba a rasa ba."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng