Tallafin ruwan leda: Jama'a sun caccaki uwargidan gwamnan Bauchi

Tallafin ruwan leda: Jama'a sun caccaki uwargidan gwamnan Bauchi

Aishatu Mohammed, uwargidan gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ta shiga bakin jama'a bayan da ta raba jaka-jaka na ruwan leda a matsayin kayan tallafi ga matan kauyen Futuk da ke karamar hukumar Alkaleri.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, ta raba wa matan don tallafi da dogaro da kai ne.

Abubuwan da ta raba sun hada da injin taliya, fulawa, ruwan leda da kuma N5,000 ga mata 250.

Ta raba kayayyakin ne karkashin jinjirar gidauniyarta mai suna "Almuhibbah".

Amma kuma ruwan leda da ta raba ya janyo cece-kuce daga ma'abota amfani da kafar sada zumuntar zamani.

Dubban jama'a sun yi tofin Alla-wadai ga uwargidan gwamnan bayan yaduwar hotunan.

A hotunan, an ga mata na layi inda suke karbar ruwan leda wanda aka ajiye a kasa.

Wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani na Facebook, Oyedokubo Oladayo, ya ce: "wannan rashin hankali ne. Nawa ruwan leda yake har da za a ce an tallafawa mata da shi. Allah ya taimakemu."

Musa Dalhatu ya rubuta: "Wannan abun takaici ne. Nawa matan nan suka saka don kudin motar da ya kaisu wurin ballantana kuma na komawa gida?

"Gaskiya sun kashe kudin da ya fi wanda aka basu. Me yasa suke haka?"

Tallafin ruwan leda: Jama'a sun caccaki uwargidan gwamnan Bauchi
Tallafin ruwan leda: Jama'a sun caccaki uwargidan gwamnan Bauchi. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Katsina: Yadda magidanci ya kashe amaryarsa ya jefa gawarta a rijiya

Okekemi Aswale Adediran a wallafarta tace: "Goben nan za ka ji an ce miliyan 100 aka kashe wurin siyan ruwan ledar nan."

Amita Judith kuwa cewa tayi: "Wannan ne abinda muka samu daga jama'a da muka sadaukarwa rayukanmu. Wannan abun kunya ne. Ka duba fa, uwargidan gwamnan jihar Bauchi ce take tallafawa mata don dogaro da kai."

Amma kuma a martanin gaggawa da sakatariyar yada labarai ta uwargidan gwamnan, Murjanatu Maidawa tayi, ta ce hotunan ruwan leda da aka yada a kafafen sada zumuntar zamani an yi su ne don tozarta uwardakinta.

Ta kara da wallafa hotunan masu bada takaici inda wasu ke cewa ruwan leda kadai aka raba.

Maidawa ta zanta da jaridar The Nation inda tace sun raba injin murza taliya, fulawa da N5,000 ga mata N250 don su samu jarin kansu.

Ta ce basu bada ruwan leda don tallafi ba, illa iyaka don amfanin wadanda suka je karbar tallafin.

Ta ce uwardakinta ta bada leda 20 ta ruwan ledan don amfanin mata da maza da suka halarci wurin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: