Yan da zaka sarrafa bolar gidanka ta dinga kawo maka kudi

Yan da zaka sarrafa bolar gidanka ta dinga kawo maka kudi

Wata kungiya mai kula da gyaran muhalli ta fito da wata hanya ta amfani da bola, wurin samarwa da yara hanyar biyan kudaden makarantarsu

A yadda kungiyar ta tsara shine, duk lokacin da iyaye su ka kawo robobi da darajarsu ta kai rabin kudin makarantar yaro, to kungiyar za ta biya rabi, sai iyayen su biya rabi.

A Najeriya akan yi wa jarirai amfani da kunzugu ko nafkin wanda aka yi shi da roba, kenan hakan na nufin an fara tara kilo daya na bola a duk rana.

"Sunana Olufunto Buroffice kuma ni ce na kirkiro da kungiyar Chanja Datti da ke kwashe shara da kuma juya sharar zuwa abu mai amfani.

Yan da zaka sarrafa bolar gidanka ta dinga kawo maka kudi
Yan da zaka sarrafa bolar gidanka ta dinga kawo maka kudi
Asali: UGC

"A nan mu kan juya tsakanin tan 100 zuwa 200 na shara a kowanne wata. Muna da ma'aikata mata da maza fiye da 80 da suke yi mana aiki a nan.

"Muna sarrafa ledojin ruwa zuwa maballai, su kuma wadannan maballan, ana amfani da su wajen sarrafa abubuwa kamar ledojin shara da kwanon rufin gida. Muna nike wasu robobin, sannan kuma masu yin buta da silifas su kan zo wajenmu sayen kayayyaki.

KU KARANTA: An kashe wata 'yar Najeriya da aka kama tana safarar kwayoyi a Saudiyya

"Muna da wani tsari na musayar bola da litattafai domin tabbatar da cewa yara suna makaranta, inda mukan ce, idan za ku iya kawo bola, to ita ce rabin kudin makarantar yaro, su kuma iyaye sai su biya ragowar kudin makarantar.

"Muna ganin yana da muhimmanci sosai mu mayar da sarrafa bola ya zame mana al'ada."

Wannan wata dama ce ga iyaye musamman ma wadanda ba su da karfi sosai wurin biya wa yaransu kudin makaranta su yi amfani da wannan damar domin ragewa kansu nauyin karatun yaransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng