IDGC: Tajuddeen Abbas Ya bar Kujera, An Samu Sabuwar Shugabar Majalisar Wakilai
- Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen ya kafa tarihi a zauren majalisar yayin da ake bikin ranar 'ya'ya mata ta duniya ta 2024
- An ce Rt. Hon. Abbas Tajudeen ya sauka daga kan kujerarsa, inda ya dora 'yar shekara 16 a matsayin shugabar majalisar ta wucin gadi
- Da take magana a matsayin shugabar majalisar wakilai ta wucin gadi, Ms Isabel Anani ta ce tana fatan 'ya'ya mata su samu daidaito
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Majalisar wakilai ta gudanar da bikin ranar 'ya'ya mata ta duniya na shekarar 2024 a cikin wani salo da ya ja hankalin jama'a a ranar Alhamis, 10 ga Oktoba.
Shugaban majalisar, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ya kafa tarihi ta hanyar sauka daga kujerarsa tare da dora Ms Isabel Anani mai shekaru 16 da ke fafutukar daidaiton jinsi.
'Yar shekara 16 na hau kujerar shugabar majalisa
Rahoton Arise TV ya nuna cewa Ms Isabel Anani ta dare kan kujerar shugaban majalisar na wucin gadi a wani yunkuri na nuna makomar 'ya'ya mata a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar, Akin Rotimi Jr., ya fitar yayin zaman ya ce shugaban majalisar, Hon. Abbas ya bayyana cewa:
"Ina kira ga sauran 'yan majalisa da su taya ni tafawa Isabel da sauran yara mata na Najeriya bisa ci gaba da suke yi wajen nuna kwazo da kokarin cimma muradunsu."
Sanarwar da aka wallafa a shafin majalisar na X ta ce Rt. Hon. Abbas ya ce babu wani shugaban majalisa da ya taba yin irin haka, wanda ke nuna goyon bayansa ga ci gaban 'ya'ya mata.
'Yar shekara 16 ta yi wa majalisa jawabi
Shugabar majalisar wucin gadi, Isabel Anani, wadda aka zaba daga cikin jerin 'ya'ya mata a fadin Najeriya, ta bayyanawa majalisar wakilan cewa:
"Ina fatan kowace yarinya za ta samu damar bunƙasa, a inda ba a kallon ilimi a matsayin wani ginshiki zai ba ‘yan mata damar yanke hukunci kan abin da ya shafe su."
Isabel Anani ta kuma ce tana fatan 'ya'ya mata za su samu daidaito a makomarsu yayin da za su yi gogayya da 'ya'ya maza wajen ilimi da samun damarmaki.
Sanata Akpabio zai yi murabus a majalisa?
A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar dattawa ta mayar da martani ga jam'iyyar PDP kan kiran da ta yi na cewa Sanata Godswill Akpabio ya sauka daga shugaban majalisar.
Shugaban kwamitin yada labarai, Yemi Adaramodu, ya ce Akpabio ba zai sauka daga shugabancin majalisar dattawa ta 10 kamar yadda PDP ta bukata ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng