Ku yiwa 'ya'ya Mata kyakkyawar tarbiya - Imamu Bako

Ku yiwa 'ya'ya Mata kyakkyawar tarbiya - Imamu Bako

Shugaban Limaman babban Masallacin Ajegunle da ke jihar Legas, Isma'il Owolabi Bako, ya yi gagarumar huduba akan sanya idanun lura tare da bai wa 'ya'ya Mata kyakkyawar tarbiyya tun su na kananan shekaru na kuruciya.

Ku yiwa 'ya'ya Mata kyakkyawar tarbiya - Imamu Bako

Ku yiwa 'ya'ya Mata kyakkyawar tarbiya - Imamu Bako
Source: UGC

Babban Limamin ya yi kira na neman iyaye su yiwa 'ya'yayen su Mata kyakkyawar tarbiya tare da ba su kulawa musamman tun daga shekaru 10 na haihuwa har zuwa su mallaki hankali da a cewar sa hakan zai kawo sauki matuka wajen cin zarfin su da keta masu haddi a fadin kasar nan.

Yayin kira na neman dagewa wajen tarbiyar 'ya'ya Mata daga shekaru 10 har zuwa 40, Liman Bako ya shawarci iyaye da su haramtawa 'ya'yan su mu'amala da kuma cudanya ta gaira ba bu dalili a tsakanin su da kishiyoyin jinsi.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, babban Limamin ya yi wannan gagarumar huduba yayin gabatar da jawaban sa a taron wayar da kai a kan cin zarafin Mata da kungiyoyin duniya tare da Ma'aikatar shari'a suka nauyin gudanarwa a babban Masallacin Ajegunle na jihar Legas.

Ya kuma yi kira na neman iyaye su tarbiyyantar da 'ya'yan su Mata wajen tsare budurcin su har zuwa lokacin aure da hakan zai taimaka matuka wajen rage aukuwar fyade da kuma keta masu haddi.

KARANTA KUMA: A fara laluben watan Sha'aban a ranar Juma'a - Sarkin Musulmi

Cikin na ta jawaban, shugabar gidauniyar Cece Yara mai kula da kare hakkin Mata, Grace Ketafe, ta yi kira na neman tsira da cututtuka da ake kamuwa da su ta hanyar saduwa da kuma tozali a kan illolin cikin shege a tsakanin kananan 'yan Mata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel