Ilmantar da 'ya'ya mata shine mabudin cigabanmu baki daya - Sanusi Lamido

Ilmantar da 'ya'ya mata shine mabudin cigabanmu baki daya - Sanusi Lamido

- Tsohon sarkin Kano kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Lamido Sanusi, ya sanar da ra'ayinsa game da ilimin 'ya'ya mata

- Kamar yadda yace, matukar al'umma na son dawwama a farin ciki, cigaba da nasarori, dole ne a bai wa yara mata ilimi

- Tsohon basaraken ya sanar da hakan ne yayin kaddamar da wani sabon shiri na malaman makaranta

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Lamido Sanusi ya bayyana matsayarsa a kan karatun 'ya'ya mata wanda yace shine jigon cigaban kowacce al'umma.

Sanusi ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin kaddamar da wani sabon shirin cigaba ga malaman makaranta a kasar nan. Ya yi bayanin cewa shirin zai samar da damar inganta ilimi tare da bai wa mata da kananan yara damar samunsa a yankunan da rikici yayi kamari.

Ya bayyana cewa, shirin ya samu tallafi daga kasar Canada domin inganta neman ilimi tare da bai wa marasa karfi damar samunsa.

"Ilimi shine mabudin cigaban kowacce al'umma. Dole ne mu cigaba da bashi fifiko saboda shine jigon komai.

"Muna daga cikin al'umma masu yawa, farin cikinmu, nasararmu da cigabanmu ba zai yuwu ba sai da ilimi.

"Ina da tabbacin cewa ilimantar da 'ya'ya mata zai kawo karshen mace-macen kananan yara, talauci kuma ya samar da ingantacciyar rayuwa ga al'umma," yace.

Sanusi wanda shine babban shugaban jami'ar jihar Kaduna, ya ce malamai masu matukar kwarewa za su iya zama tushen cigaba kuma za su iya kawo sauyi a al'umma.

KU KARANTA: Cutata aka yi, ashe tana da 'ya'ya uku na aureta - Magidanci ya sanar da kotu

Ilmantar da 'ya'ya mata shine mabudin cigabanmu baki daya - Sanusi Lamido
Ilmantar da 'ya'ya mata shine mabudin cigabanmu baki daya - Sanusi Lamido. Hoto daga Channels TV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda 'yan sanda suka azabtar da matashi har ya sheka lahira a Nasarawa

A wani labari na daban, Muhammadu Sanusi, tsohon sarkin Kano, ya ce bashi da wani buri na fitowa takarar kujerar siyasa a kasar nan.

A yayin da zaben 2023 ke gabatowa, ana ta hasashen 'yan takara da za su bayyana kafin zaben. A wata tattaunawa da basaraken ya yi da Arise TV a ranar Juma'a, Sanusi ya ce bashi da ra'ayin siyasa kwata-kwata.

Tsohon basaraken ya ce zai koma karatu a fitacciyar jami'ar Oxford da ke Ingila a watan Oktoba mai zuwa.

Hukumar kwamitin cibiyar Afrika ta makarantar, ta amince da bukatar Sanusi na komawa karatun. Tsohon basaraken ya ce yana da niyyar komawa malumta, wanda daga nan ya fara rayuwarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel