Gwamnatin Najeriya Za Ta Hukunta Attajirin Duniya Elon Musk, Bayanai Sun Fito
- Gwamnatin Najeriya na shirin hukunta attajirin duniya, Elon Musk kan kara kudin da 'yan Najeriya ke biya wajen amfani da Starlink
- An ce kamfanin Elon Musk ya kara kudin da ya ke cajar 'yan Najeriya duk wata na amfani da Starlink daga ₦38,000 zuwa ₦75,000
- Gwamnati ta ce matakin da Starlink ya dauka ba tare da sahalewarta ba ya saba da sashe na 108 da 111 na dokar sadarwa ta Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta sanar da cewa za ta dauki matakin tabbatar da doka da oda a kan tashar sadarwar tauraron dan adam ta Elon Musk, Starlink.
Hukumar NCC na shirin daukar matakin ne biyo bayan aiwatar da karin farashin amfani da Starlink da Elon Musk ya yi a Najeriya ba tare da izini ba.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa daraktan hulda da jama’a na hukumar NCC, Reuben Muoka, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Elon Musk ya kara kudin Starlink
Reuben Muoka, ya bayyana cewa kamfanin Starlink ya kara kudin da yake karba na wata-wata daga ₦38,000 zuwa ₦75,000 (karin 97%).
Haka kuma farashin kayan kafa na'urar Starlink ya yi tashin gwauron zabi, wanda ya karu da kashi 34 zuwa ₦590,000 daga ₦440,000, inji wani rahoto na The Punch.
Kamfanin Elon Musk ya sanar da abokan cinikinsa canje-canjen a makon da ya gabata, inda ya ce karin kudin zai shafi tsofaffi da sababbin abokan huldarsa.
Gwamnati za ta hukunta Elon Musk
Sai dai kuma hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya ta fayyace cewa ba ta amince da sauye sauyen da Starlink ya yi ba.
"Shawarar da Starlink ta yanke na kara kudin data da masu amfani da fasahar ke biya bai samu amincewar hukumar sadarwa ta Najeriya ba.
"Matakin da kamfanin ya dauka ya sabawa sashe na 108 da 111 na dokar sadarwa ta Najeriya (NCA) 2003, da sharuɗɗan lasisin da aka ba Starlink game da haraji."
- A cewar Reuben Muoka.
Sashe na 111 na dokar ya ba hukumar NCC damar kakaba tara ga masu lasisin da suka wuce adadin kudin da aka amince masu.
Elon Musk zai kafa Starlink a Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa SpaceX, wani kamfanin Elon Musk ya nemi sahalewar gwammati domin fara samar da intanet dinsa mai suna Starlink a Najeriya.
Wakilan kasuwancin Afirka na SpaceX, Ryan Goodnight ne ya bayyana haka, yayin wata tattaunawa da shugaban hukumar sadarwa ta kasa (NCC), Farfesa Umar Danbatta.
Asali: Legit.ng