Bello Turji Ya Saki Sabon Bidiyo, Ya Kafa Sharudan Zaman Lafiya a Zamfara
- Hatsabibin jagoran 'yan bindiga, Bello Turji ya sake fitar da sabon bindiyo inda ya kafawa gwamnati sharadin zaman lafiya a Zamfara
- Bello Turji wanda ya ce ya dauki bidiyon a ranar 30 ga Oktoba ya ce hare-haren sojoji da 'yan banga ba shi zai sa su daina kashe mutane ba
- Game da rikicin da ake yi tsakanin Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal da Bello Matawalle, dan ta'addan ya ce an siyasantar da ta'addanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara - Jagoran 'yan bindiga, Bello Turji, ya ce gwamnan Zamfara, Dauda Lawal da magabacinsa Bello Matawalle suna siyasantar da rashin tsaro a jihar.
Bello Turji, wanda ake kyautata zaton ya tsere daga Zamfara bayan da sojoji suka zafafa kai hare-hare kan ‘yan ta’adda a jihar, ya ba da sharudan samar da zaman lafiya a jihar.
Sabon bidiyon Bello Turji
Kasurgumin shugaban 'yan bindigar ya kafawa gwamnati sharudan zaman lafiyar ne a wani faifan bidiyo da ya fitar wanda wani Habibu Bello Maiyama ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin faifan bidiyon, an ga Bello Turji ya na zaune a kan wani sabon babur dauke da bindiga. A gefe kuma ga wata bindigar da ake tunanin ta wanda ke daukarsa bidiyon ce.
Bello Turji ya ba da sharadin zaman lafiya
Bello Turji ya ce ya dauki bidiyon ne a ranar 30 ga watan Satumba, kuma ya yi magana ne kan jihar Zamfara yana mai jaddada cewa ba sa tsoron mutuwa.
Dan ta'addan ya ce zaman lafiya zai dawo Zamfara idan jami’an tsaro da ’yan banga suka daina kai hare-hare da kashe Fulani a jihar da sauran wurare.
"Ba ma tsoron a kashe mu, ba ma tsoron a jefa mana bam. Amma ina maimaita maku matsayarmu, idan aka daina kashe mana mutane, za mu daina kisa mu ma.
"Idan kuna son magance matsalar tsaro, ku koma baya, ku tuna tun zamanin Ahmad Yariman Bakura kuka sare mana dajujjuka, kuka halatta jinin Fulani, ana kashe mu.
"Saboda haka muke kira da mu zo mu hada kai mu bar kashe al'ummar jihar Zamfara, amma mu barazana ba za ta tsorata mu ba, da ma mun shirya mutuwa."
Turji ya soki Dauda da Matawalle
Bello Turji ya ce zarge zargen da ake yi tsakanin Gwamna Dauda Lawal da ministan tsaro, Bello Matawalle, siyasa ce kwai inda ya ce ‘yan siyasar biyu ba su damu da jama'arsu ba.
"Ina kira gareku al'ummar Zamfara, su sun gwada maku su 'yan siyasa ne ba al'umma ne a gabansu ba. Mu babu mai daukar nauyinmu sai Allah.
"Lokacin da Abdulaziz Yari na gwamna, Matawalle ne ke daukar nauyinmu? Lokacin da Matawalle na gwamna, Dauda ne ke daukar nauyinmu? Ku tsaya ku yi nazari."
Bello Turji ya jadadda cewa har sai an daina kashe Fulani a Katsina, Zamfara, Sokoto da Neja ne za a dawo da zaman lafiya a yankunan.
Duba bidiyon a kasa:
Bello Turji ya tura sako ga Janar Christopher
A wani labarin, mun ruwaito cewa hatsabibin dan bindiga, Bello Turji ya roki babban hafsan tsaron Najeriya Christopher Musa da ya ba Sheikh Murtala Bello Asada mukami.
Bello Turji ya nemi a ba malamin mukamin soja ko shugaban 'yan banga saboda ya shiga daji su gwabza yaki tsakaninsu bayan maganganun da malamin ya yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng