Kasurgumin Ɗan Bindiga, Bello Turji, Ya Rungumi Zaman Lafiya a Zamfara, Mataimakin Gwamna

Kasurgumin Ɗan Bindiga, Bello Turji, Ya Rungumi Zaman Lafiya a Zamfara, Mataimakin Gwamna

  • Mataimakin gwamnan Zamfara, Hassan Nasiha, ya ce ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji, ya rungumi shirin zaman lafiya
  • Kwamitin da gwamna Matawalle ya kafa ya zauna sulhu da kungiyoyin yan bindiga Tara a kananan hukumomi uku
  • Gwamnatin Zamfara na cigaba da kokarin bin kowace hanya domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar

Zamfara - Shahararren shugaban yan bindiga, Bello Turji, ya rungumin shirin zaman lafiya da gwamnatin jihar Zamfara ta zo da shi a wani ɓangaren koƙarin kawo karshen ayyukan yan bindiga a jihar.

Mataimakin gwamnan Zamfara, Sanata Hassan Nasiha, shi ne ya bayyana haka a wurin wani taro kan tsaro da ƙunguyar Ɗaliban jami'ar Madinah suka shirya a Gusau, babban birnin jihar.

Sanata Nasiha ya yaba wa ƙasurgumin ɗan bindiga Turji bisa ɗaukar matakin aje makamansa, kamar yadda jaridar Channesl tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kakakin Majalisar Kaduna Ya Magantu Kan Shirin Tsige Gwamna El-Rufai

Bello Turji ya rungumi zaman lafiya.
Kasurgumin Ɗan Bindiga, Bello Turji, Ya Rungumi Zaman Lafiya a Zamfara, Mataimakin Gwamna Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Mataimakin gwamnan ya ƙara da cewa Matakin Bello Turji ya taimaka wajen dawowar zaman lafiya a yankunan ƙananan hukumomi uku, waɗan da kafin haka sune sahun gaba a ta'addancin yan fashin daji a Zamfara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Sanata Masiha, a mako biyar da suka gabata, ba'a sake jin ɗuriyar rikicin Fulani da Hausawa ba a kananan hukumomin Birnin Magaji, Shinkafi da Zurmi.

Hakan ta faru ne sakamakon tattaunawar masalaha da zaman lafiya tsakanin ɓangarorin biyu da basu ga maciji da juna a jihar, a bayaninsa.

"Duba da haka ne mai girma gwamna Bello Matawalle ya yi tunanin ya dace a bi hanyoyi da dama, bai kamata ya tsaya a musayar wuta da bindigu ba ko yaƙi da kowane irin makamai tsakanin yan fashin daji da mutane."

Mun zauna da tawagar yan bindiga Tara - Nasiha

Kara karanta wannan

'Suna Shirin Kashe Ni' Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya Ya Aike da Sako Ga IGP, Ya Fallasa Sunaye

Bugu da ƙari, ya bayyana cewa kwamitin da gwamna ya naɗa kuma ya ɗora shi a matsayin shugaba ya zauna taron sulhu da ƙungiyoyin yan ta'adda Tara (9) a yankin Magami, Masarautar Ɗansadau, da Maru domin su daina kaiwa mutane hari.

"Wannan ne dalilin da yasa a watanni uku da suka wuce a Magami, ba'a ji yan bindiga sun kai hari ba sakamakon shirin zaman lafiya. Kwamiti ya gana da tawagar yan ta'adda Tara kuma sun faɗi damuwarsu."
"Sun ce Hausawa na kai musu farmaki suna cin zarafin matan su, suna kashe Fulani a hanyar komawa gida daga Kasuwa. Ba'a gina mana makaranta da yaran mu zasu rinka zuwa ba, shiyasa suke shiga fashi."

- Nasiha

Abinda Turji ya koma yi a yanzu - Mataimakin Matawalle

Mataimakin gwamnan ya kara da cewa Turji, wanda ya zama ƙusa a shirin sulhu na gwamna Matawalle, ya komayaƙar yan ta'adda domin tabbatar da zaman lafiya ya samu gindin zama a jihar, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Na Yi Alkawarin Kuɗi N50,000 Ga Duk Wanda Ya Fallasa Bayanan Yan Bindiga a Jihata, Gwamnan APC

A wani labarin kuma Yan bindiga sun sake kai kazamin hari Garuruwa Takwas a jiha arewa, rayuka sun salwanta

Aƙalla mutum uku aka tabbatar sun rasa rayukansu bayan wasu miyagun yan bindiga sun aikata mummunan ta'addanci a ƙauyen Zagi da wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Augie, jihar Kebbi.

A ruwayar hukumar Dillancin labarai ta ƙasa (NAN), harin da yan bindigan suka kai ranar Laraba ya bar mutane da dama kwance a Asibiti suna karɓan magani, yayin da aka sace wasu 15.

Asali: Legit.ng

Online view pixel