Gwamnatin Shiyya: An Samu Baraka Tsakanin Sanatoci kan Bitar Kundin Tsarin Mulki

Gwamnatin Shiyya: An Samu Baraka Tsakanin Sanatoci kan Bitar Kundin Tsarin Mulki

  • A karshen mako ne sanatoci suka hadu a Kano kan yiwa kundin tsarin mulki garambawul inda suka yi muhawara kan tsarin siyasar Najeriya
  • Yunkurin komawa mulkin yanki, wanda aka fara yinsa tun a jamhuriya ta farko, ya haifar da rashin jituwa a tsakanin ‘yan majalisar
  • Masana dai na ganin cewa aikin yiwa kundin tsarin mulkin kasar garambawul ya fallasa barakar akidar da ke tsakanin 'yan majalisar dattawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Kwamitin majalisar dattawa kan sake duba kundin tsarin mulki na 1999 ya gudanar da wani taro a jihar Kano a karshen makon nan.

Sanatocin Najeriya sun bayyana mabambantan ra'ayoyi game da yunkurin sake dawo da tsarin mulkin shiyya da fara yinsa a kasar a lokacin jamhuriya ta farko.

Kara karanta wannan

NAGGMDP: Likitoci za su tsunduma yajin aiki a jihar Kano, bayanai sun fito

An samu sabani a majalisar dattawa kan tsarin mulkin Najeriya
Gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya ya jawo sabani tsakanin sanatoci. Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Muhawarar sauya tsarin mulki

Yayin da wasu sanatoci ke cewa komawa mulkin yanki zai ba jihohin tarayya damar tattala dukiyarsu, wasu kuma sun dage cewa tsarin mulkin na yanzu ba shi da matsala, inji rahoton Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana da manema labarai, sanata mai wakiltar Oyo ta Arewa, Abdulfatai Buhari ya bayyana cewa:

"Idan aka koma gwamnatin yanki, zai taimaka sosai wajen dakile cin hanci da rashawa kuma hakan zai sa gwamnatin tarayya ta rage karfin iko kan jihohi.
“Babu wani rinjaye na takamaiman albarkatu a lokacin mulkin yanki. An san Arewa da dalar gyada an san Kudu da noman cocoa, don haka wannan tsari ne da zai haifar da da mai ido."

"Babu mazabata a ciki" - Ningi

Sai dai sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya, Abdul Ningi ya yi watsi da wannan kudiri, domin ya ce babu ruwan mazabarsa da komawa mulkin shiyya.

Kara karanta wannan

Garambawul: Tinubu zai sallami ministoci 11 da wani babban jami'in gwamati

"Al'ummar mazabata ba su ji dadin gwamnatin shiyya ba a wancan lokaci da ta ke Kaduna. Ba za mu sake komawa wancan tsarin ba, ina magana a madadin 'yan mazabata."

- A cewar Sanata Ningi.

"Mu tattauna a baki kawai" - Bamidele

Shugaban masu rinjaye, Michael Opeyemi Bamidele ya bayyana ra'ayinsa game da yuwuwar watsi da kundin tsarin mulkin da ake da shi yanzu tare da shirya sabo dal.

"A mahangata, mu tattauna kan batun komawa tsarin mulkin shiyya, amma ka da mu dauki wani mataki na majalisa a kai saboda abu ne wanda ke da kamar wuya."

- A cewar Sanata Bamidele.

Sanata Dandutse ya shiga tsakani

Sanata mai wakiltar Katsina ta Kudu, Sanata Muntari Dandtuse ya ce abin da ke da muhimmanci shi ne kyakkyawan shugabanci.

Sanata Dandutse ya ce:

"Ya kamata mu kasance masu hangen nesa. Idan muna maganar albarkatun kasa, to babu wani yanki da ba shi da albarku. Abu mai muhimmanci shi ne kyakkyawan shugabanci."

Kara karanta wannan

Cin hancin N15m: Majalisar wakilai ta gayyaci shugaban EFCC da wasu mutum 2

Za a yi sauye sauye a kundin mulki

A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar tarayya ta tsayar da watan Disambar 2025 a matsayin wa'adin kammala aikin bitar kundin tsarin mulki na 1999.

An rahoto cewa majalisar a halin yanzu tana aiki kan wasu kudirori 40 da ke kan matakai daban-daban da suka shafi sauya kundin tsarin mulkin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.