Gwamnatin Tinubu: Shugabannin Tsaro 15 na Najeriya da Jihohin da Suka Fito

Gwamnatin Tinubu: Shugabannin Tsaro 15 na Najeriya da Jihohin da Suka Fito

  • Tawagar tsaro ta Shugaba Bola Tinubu karkashin jagorancin NSA Nuhu Ribadu, ta fito ne shiyyoyin siyasar kasar nan guda shida
  • Wani bincike kan tawagar ya nuna cewa Tinubu ya nada kimanin mutane 15 a matsayin shugabannin hukumomin tsaro daban-daban
  • Najeriya dai na fuskantar matsalar tabarbarewar tsaro, inda ake fama da tashe-tashen hankula daga ayyukan 'yan ta'adda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki, ya gaji matsalar rashin tsaro da ta ke addabar kasar nan. Ba a jima ba ya kaddamar da tawagar shugabannin tsaronsa.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, shi ne ke jagorantar tawagar tsaro ta Bola Tinubu, wanda a lissafi ta kunshi shugabannin tsaro 15, ciki har da hafsoshin sojoji.

Kara karanta wannan

"Za mu kai dauki Maiduguri": Tinubu ya aika sako ga Zulum bayan ambaliyar ruwa

Nuhu Ribadu ke jagorantar tawagar tsaron Shugaba Bola Tinibu ta mutane 15
Cikakkun jerin 'yan tawagar tsaro da ke aiki tare da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: @officialABAT, @NuhuRibadu, @PoliceNG
Asali: Twitter

Najeriya dai na fuskantar matsalar tabarbarewar tsaro, inda ake fama da tashe-tashen hankula da ayyukan 'yan ta'adda daban daban a fadin kasar.

Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya

Rikicin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas ya yi sanadiyyar mutuwar dubunnan mutane da lalata muhallansu da kuma take hakkin dan Adam.

Baya ga barazanar Boko Haram, Najeriya na fama da matsalar ‘yan bindigar daji, masu garkuwa da mutane, da fashi da makami.

Nuna ikon mallakar gonaki da muhalli ya jawo gaba mai tsanani tsakanin makiyaya da manoma wanda ya haifar da kazamin fadan da ya yi sanadin ajalin mutane da dama.

Matsalar tsaro a Kudancin Najeriya

Yankin Neja-Delta na fuskantar kalubalen tsaro na musamman da suka hada da tsagerun Neja-Delta, 'yan fashin teku da barayin mai.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kadu da ambaliyar ruwa a Maiduguri, ya ba Shettima sabon umarni

Rashin zaman lafiya a yankin dai ya yi tasiri matuka ga tattalin arzikin kasar, kasancewar a yanki ne ake hako man da ke tafiyar da tattalin kasar.

Kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ta dade tana fafutukar neman ballewa a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, domin neman ‘yancin kai ga al’ummar Biafra.

Ayyukan kungiyar ta IPOB na zama a gida da kuma daukar kudirin neman cin gashin kansu, da rikicinsu da jami'an tsaro, ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.

Tawagar tsaron Shugaba Tinubu

Legit.ng ta tattaro jerin 'yan tawagar tsaron shugaban kasa Bola Tinubu, duba jerin a kasa:

S/NSunaMatsayiJiha
1Badaru AbubakarMinistan tsaroJigawa
2Bello MatawalleKaramin ministan tsaroZamfara
3 Olubunmi Tunji-OjoMinistan cikin gidaOndo
4Ibrahim GaidamMinistan 'yan sandaYobe
5Nuhu RibaduMai ba shugaban kasa shawa kan tsaro (NSA)Adamawa
6Taoreed Lagbaja Shugaban hafsan sojan kasaOsun
7Christopher MusaBabban Hafsan TsaroKaduna
8Hasan AbubakarShugaban hafsan sojan samaKano
9Emmanuel OgallaShugaban hafsan sojan ruwaEnugu
10Kayode EgbetokunBabban sufetan 'yan sandaOgun
11Bashir A AdeniyiShugaban hukumar kwastamOsun
12Adeola O AjayiShugaban hukumar DSSOsun
13Mohammed MohammedShugaban hukumar NIAKwara
14Ahmad A AudiShugaban hukumar NSCDCNasarawa
15Kemi N NandapShugabar hukumar shige da ficeKaduna

Kara karanta wannan

'Babu ruwanmu' APC ta barranta daga maganar takarar Tinubu a 2027

Gwamnoni sun dauki mataki kan tsaro

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnonin Arewa maso Yamma sun amince da wani tsari da wa'adi na kawo karshen matsalar rashin tsaro da ta addabi shiyyar.

A cewar Gwamna Dikko Radda, tsarin da aka amince da shi zai sa kowane gwamna ya aiwatar da dabarun magance tsaro da aka amince da su a wajen taron da suka gabatar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.