Yadda za a kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya - Ganduje ya bawa FG shawara

Yadda za a kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya - Ganduje ya bawa FG shawara

- Har yanzu al'amuran tsaro sun gaza daidaituwa a Najeriya, musamman a yankin arewa

- Jihar Kano na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke zaune lafiya ba tare da manyan kalubale a bangaren tsaro ba

- Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana irin kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen tabbatar da tsaro a jihar Kano

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da muhimman shawarwari a kan yadda za a kawo karshen kalubalen matsalar tsaro a Najeriya.

A cewar Ganduje, gwamnati za ta iya shawo kan matsalar tabarbarewar tsaro ta hanyar amfani da sabon ilimin fasahar sarrafa bayanai (ICT), amfani da 'yan sandan cikin al'umma da kuma hada gwuiwa tsakanin hukumomin tsaro.

Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da ya ke gabatar da wata takarda a kan yadda za a inganta tsaro domin habaka tattalin arziki a wurin wani taro na manyan shugabannni da cibiyar NISS (National Institute for Security Studies) ta shirya a Abuja.

KARANTA: Wadatar da kasa da abinci: Buhari ya zabtare farashin taki a Nigeria

Yayin taron, wanda aka yi a Bwari, Ganduje ya bayyana cewa; "manufar tsaro shine kare rayukan jama'a, dukiyoyinsu da na hukuma domin tabbatar da dorewar cigaban tattalin arzikin kasa.

"Tsaro da cigaban tattalin arzikin kasa suna tafiya kunnen doki, shi yasa babu wata al'umma da zata samu cigaba idan babu tsaro.

Yadda za a kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya - Ganduje ya bawa FG shawara
Buhari da Ganduje Tuwita - @dawisu
Asali: Twitter

"Tsaro shine babban kalubale a kasar nan. Shi yasa zan yi magana a kan yadda mu ka tunkari matsalar tsaro a Kano a yayin da ma su aikata laifuka ke kara yawa da bullo da sabbin dabaru.

"A kokarinmu na shawo kan matsalar garkuwa da mutane da sauran laifuka, gwamnatinmu ta rungumi amfani da ICT; yanzu haka mu na da na'urorin sirri na bincike da bin diddigi, wadanda babu wata jiha da ke da irinsu a Najeriya.

KARANTA: Mutuwar Sarakunan Borno guda biyu a lokaci daya ya girgiza ni - Buhari ya magantu

"Bayan haka, mun mayar da hankali wajen daukan matakan tabbatar da tsaro a tsakanin jama'a. Mun kafa cibiyoyi da kwamand a wurarare daban-daban da ke kusa da jama'a domin gaggauta mayar da martani yayin rikici ko husuma da kuma kiyaye faruwar duk wani abu da kan iya tayar da hankalin jama'a," kamar yadda gwamnan ya bayyana.

Ko a kwanakin baya saida Legit.ng Hausa ta wallafa rahoto a kan yadda jami'an tsaro ke kallon motsin mutane da ababen hawa a manyan titunan birnin Kano ta hanyar amfani da boyayyun na'urorin sa-ido.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel